Gwamnati Kaduna ta bada hutun kwana daya domin yi wa marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris addu’oin Allah yayi masa gafara.
Marigayi sarki Shehu, zai cika kwanaki uku da rasuwa ranar Laraba, wanda a wannan rana ne gwamnati ta ce kowa ya zauna a gida domin yin jimamin rasuwar marigayin da kuma yi masa addu’oi.
Bayan haka gwamnati ta ce tun daga ranar Litini ne za a fara wannan zama na jimami amma kuma, ba zai hana ma’aikata zuwa wuraren aikin su ba, sai dai ranar laraba ce ba za a tafi aiki ba.
Sannan kuma sanarwar wanda kakakin gwamna El-Rufai, Muyiwa Adekeye ya saka wa hannu, ya ce za a sassauke tutocin zuwa kasa, har sai ranar Alhamis.