Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa Boko Haram sun taba yi masa kwanton Bauna a cikin 2015, inda ya kubuta da kyar-da-gumin-goshi.
Buratai ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke bude gadar da sojoji su ka gina a garin Kuta, Jihar Osun a ranar Litinin.
Gadar dai bangaren Sojojin da ke aikin Injiniya da Gine-gine ne, wato Nigeria Army Engineering Construct Regiment da ke Ede ne suka gina ta.
An sa wa gadar suna Buratai, kamar yadda sojoji ke yawan sa wa wasu gine-gine sunan sa.
Da ya ke magana a kan irin kaunar da ya ke wa Jihar Osun, Buratai ya ce Mataimakin sa Lamidi Adeosun, wanda dan asalin Jihar Osun ne, shi ya ceci ran sa a lokacin da Boko Haram su ka kai wa Buratai din hari.
Buratai ya ce mataimakin sa Adeosun ne ya gaggauta kai masa daukin gaggawa, tare da zaratan sojoji, a lokacin da Boko Haram din su ka yi wa Buratai kwanton-bauna, cikin 2015.
“Kwanton-baunan farko da Boko Haram su ka yi min, ina tare da shi a cikin mota ne. Na ga yadda ya nuna jarumta, ya hada zaratan sojoji su ka kori Boko Haram daga inda suka tare mana hanya.
“Lokacin da aka nada ni Babban Hafsan Sojojin Najeriya, na je na samu Lamidi Adeosun, lokacin ya na kwamandan yaki da Boko Haram. A can mu ka fara tsara nasarar durkusar da Boko Haram.”
Buratai ya gode wa Sojojin da su ka gina gadar, kuma jinjina wa Basarake Olowu na Kuta, Adekunle Oyelude, saboda goyon bayan da ya ke wa sojoji a lokacin da jama’a ke yawan sukar su.
Gwamnan Osun Gboyega Oyetola, gina gadar za ta kara karkafa dangantakar tsakanin sojojin da fararen hular Jihar Osun.
Cikin 2015 PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa sojoji sun kai wa tawagar Buratai hari, har sun kashe soja daya.