Akalla mutum 1,165 aka bindige har lahira tsakanin Janairu zuwa Agusta a yankin Arewa maso Yamma.
Wani rahoto ya tabbatar cewa an kuma yi garkuwa da akalla mutum 113 cikin wadannan watanni na Janairu zuwa Agusta din, kamar yadda Ƙungiyar Jimamin Asarar Rayukan Ƴan Najeriya (Nigeria Mourns) ta ruwaito, kuma PREMIUM TIMES ta samu kwafen rahoton tun a ranar Juma’a.
Ƙungiyar wadda ke bin diddigin kididdige yawan mutanen da suka rasa rayuka sanadiyyar kashe-kashe, ta ce ta tattara adadin mutum 1,165 din ne a jihohi bakwai.
Sannan ƙungiyar ta ƙara da cewa ta riƙa tattara adadin ne daga abin da jaridu suka buga, bayanan jami’an ‘yan sanda da kuma bayanai daga bakin dangin da aka karkashe na kusa da su.
Rahoton ya ce an fi samun asarar rayuka masu yawa a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara, a cikin watanni shida.
Ga Adadin Wadanda Aka Kashe Nan:
Kaduna mutum 468
Katsina mutum 376
Zamfara mutum 204
Sokoto mutum 96
Kano mutum 10
Kebbi mutum 1.
‘Yan bindiga suka kashe mutum 1,068, Boko Haram sun kashe mutum 5, Fulani ‘yan bindiga sun kashe 73, da sauran su.
An sace mutum 11 cikin Janairu. A cikin Fabrairu an yi garkuwa da mutum 21. Mutum 18 cikin Maris, cikin Mayu an sace mutum 7, sai Yuni kuma mutum 14, sai Yuli 14 da Agusta mitum 10.
Idan ba a manta ba, tsakiyar watan Agusta ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton cewa an kashe mutum 415 cikin watan Yuli Najeriya.
Rahoton ya ce an kashe akalla mutum 415 a kashe-kashe daban-daban a Najeriya cikin watan Yuli, kamar yadda wani rahoto da wata kungiya mai suna Nigeria Mourn ta wallafa.
Cikin Rahoton Tashe-tashen Hankula a Watan Yuli”, Nigeria Mourn, wadda aikin da ta sa gaba a kasar nan shi ne bibiya da kididdigar kashe-kashen gilla a fadin Najeriya, ta ce wannan adadi da ta lissafa, kididdiga ce ta jihohi 21 kadai daga jihohi 36 na kasar nan da Abuja.
Wannan kungiya ta kan binciki rahotannin da kafafen yada labarai sahihai suka buga, sai kuma bayanan da ta tattara daga bakin iyalai, ‘yan’uwa ko majibintan wadanda aka kashe da ba a buga rahotannin su a jaridu ba.
Rahoton baya-bayan nan da kungiyar ta buga sun nuna jihohin Barno, Kaduna da Katsina ne aka fi yi wa mutane kisan-gilla a Najeriya, a cikin watan Yuli.
Ga yadda rahoton ya lissafa yawan mutanen da aka kashe a jihohin 21 da ta kididdige:
Kaduna – 139
Barno – 113
Katsina – 80
Kogi – 17
Nasarawa – 13
Taraba – 10
Benuwai – 9
Ebonyi – 8
Zamfara – 7
Filato – 5
Edo – 2
Akwa Ibom – 2
Lagos – 2
Oyo -1
Ogun – 1
Bayelsa – 1
Delta -1
Kebbi – 1
Rahoton ya ce mutum 185 duk mahara da ‘yan bindiga ne suka kashe su. Yayin da Boko Haram suka kashe mutum 123.
Makiyaya masu dauke da manyan bindigogi sun kashe mutum 67, wasu 26 kuwa wurin rikicin kabilanci aka yi musu kisan-gilla.
An kashe mutum shida a rikicin tankiya, wasu shida kuma jami’an tsaro suka yi musu kisan gilla kafin a gurfanar da su kotu.
Akwai kuma mutum biyu da suka rasa rayukan su a hannun fadace-fadace na kungiyar asiri.
283 da aka kashe fararen hula ne, sai jami’an tsaro har 132 aka kashe.
Rahoton baya na wannan kungiya ya nuna an kashe mutum 731 a cikin watan Yuni, cikin watan Mayu kuwa an kashe mutum 356.
Yayin da ake ci gaba da yi wa jama’a kisan-gilla, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta amince ‘yan Najeriya su mallaki lasisin mallakar bindiga.
Dama kuma Sanata Kabiru Marafa ya taba yin irin wannan kira cikin 2018, a lokacin ya na Sanata mai wakiltar Zamfara.
Discussion about this post