RASHIN TSARO: Ƴan bindiga sun nausa cikin daji da alƙalai biyu a Zamfara

0

Mahara sun tare hanya suka arce da alkalai biyu na Kotunan Shari’ar Musulunci a Jihar Zamfara.

Ƴan bindigar dai sun arce da Mai Shari’a Sabi’u Abdullahi da Shafiu Jangebe ne a lokacin da su ke kan hanyar komawa Zamfara daga Jamhuriyar Nijar.

Abdullahi shi ne kuma Na’ibin Limamin Masallacin Juma’a na Usaimin da ke Gusau.

Limamin Masallacin Juma’a na Umar bin Khattab da ke Gusau, Umar Kanoma ne ya sanar da garkuwar da aka yi da alƙalan biyu, bayan an kammala Sallar Juma’a. Kuma ya yi kira da a yi musu addu’ar kuɓuta.

Sannan ya roƙi gwamnati da jami’an tsaro a ceto alƙalan daga hannun masu garkuwa da mutane.

Yayin da jami’in gwamnati ya tabbatar da sace alƙalan, amma kuma bai bayyana ko a daidai ina ce aka arce da su din ba.

Kakakin Yaɗa Labarai na Ƴan Sandan Jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai daga wayar kiran da wakilin mu ya yi masa ba, domin ya ji ƙarin bayani daga gare shi.

Har yanzu ana ci gaba da fama da rashin tsaro a Arewa. Ranar Lahadi da ta gabata ne mahara suka shiga kauyen Tungar Maje da ke kusa da Abuja, suka arce da mutane da dama.

Share.

game da Author