RASHIN NASARA: Me ya sa Messi ke saurin naɗe tabarmar-kunya? Daga Ashafa Murnai

0

Yanzu dai hankalin kowa ya rabu daga kan dan wasan kungiyar Barcelona, Leonel Messi, jin cewa ya kwance kayan sa, ya yarda zai ci gaba da wasa a ƙungiyar, akalla har zuwa watan Yunin 2021, lokacin da yarjejeniyar kwangilar sa za ta ƙare.

Kamar yadda Messi ya kware da iya lailaya kwallo, to haka kuma ya kware da iya lailaya hankulan jama’a ta hanyar karkatar da hankulan su wani waje daban, a duk lokacin da ya yi rashin nasara a wani muhimmin wasan da ya kwallafa a ran sa sai ya yi nasara.

Ba Shan kashin da Barcelona ta yi a hannun Liverpool da ci 8:2 ne karo na farko da Messi ya karkatar da mutanen duniya daga ganin laifin su kan rashin bajintar su ba.

Bayan kasar sa Ajantina ta sha kashi a hannun Jamus a wasan karshe na Cin Kofin Duniya, Messi ya fusata ya daina buga wa kasar sa kwallo. Sai daga baya aka lallashe shi ya koma.

Bayan an kori Ajantina daga gasar Cin Kofin Latin, Messi ya sake fushi nan ma, sai da aka sake bikon sa, tamkar amaryar da ta yi fushi ta tafi gida, aka je aka dawo da ita.

Kurari ko barazanar da Messi ya yi ya ce zai bar Barcelona, wa wata abin tayar da hankula ba ce, duk kuwa da cewa ta shafe shekaru birjik a Barcelona, har ta zame masa jini da jijiyoyi duka.

Messi da kan sa ya san babu wani kulob yanzu a duniya da zai cika yarjejeniyar barin Messi daga Barcelona, idan lokacin barin sa bai zo ba.

Yarjejeniya ta nuna kafin Messi ya koma wata kungiya, tilas sai shi ko kungiyar sun ajiye dala milyan 700 tukunna.

To, tunda har kungiya za a iya sayen Messi ko da dala milyan 100 ce a shekarar 2021 da yarjejeniyar za ta daina aiki, don me kuma kungiyar za ta kashe har dala milyan 700 kasa da shekara daya don kawai ta saye shi? Gaggawar me wani kulob zai yi a kan sa a yanzu?

Kungiyoyi sun san cewa yadda Messi ya shekara biyar rabon sa cin kofin Champions League a Barcelona, to don an biya Barcelona diyyar dala milyan 700 an saye shi, babbar asara ce wadda ba ta da wani bambanci da gobara. Domin ba lallai ba ne ya sake iya cin kofin a sabon kulob din da zai koma, kuma nan gaba da wahalar gaske ya kara shekaru biyar ya na wasa.

Messi ya zama jagoran ‘yan wasan Barcelona a lokacin da gwanayen ‘yan wasan da ya rika jin dadin wasa da su, irin su Andrea Iniesta, David Villa da sauran su duk sun bar kulob din. Tun tafiyar su Barcelona ba ta sake cin Kofin Champions League ba.

Shekara uku a jere ana korar Barcelona a gasar Champions League, kuma kowace ranar korar bai iya samu ya jefa kwallo ba. Haka ta faru a Roma, Liverpool da kuma wulakancin da Baryern Munich ta yi musu a Lisbon, bana a 2020.

Wane kulob ne Messi zai koma a yau, har kuma ya yi garantin a can zai iya cin kofin Champions League a shekarar 2021? Idan ya koma Manchester City ko Inter Milan ko PSG, ya warke ciwon da Baryern Munich ta ji masa, ko kuwa kara jangwalewa mikin zai yi.

Messi ya san babu wani kulob da zai iya sayen sa yanzu a 2020, saboda sharuddan da ke tsakanin sa da Barcelona. Amma a 2021 ko Aston Villa za ta iya sayen sa, idan akwai ‘yan canji a kasa.

Ya dai yi wa kan sa dabara, ya gwara kawuna milyoyin masu kallon kwallon kafa, suka manta da rashin nasarar da Barcelona ta yi, aka koma ana tattauna batun bijirewar da Messi ya yi wa kungiyar sa Barcelona.

Mu jira karshen kammala wasan sa a kungiyar cikin Juni, 2021. Kuma a lokacin za mu san ina zai dosa ne?

Share.

game da Author