Rahoton yadda cutar Korona ta talauta mutum milyan 37 talakawa fitik

0

Cutar Korona da ta barke a farkon shekarar 2020, ta maida mutum milyan 37 talakawa fitik, kamar yadda wani rahoto da Gidauniyar Tallafin Bill & Melida Foundation ta bayyana.

Gidauniyar ta ce mafi yawan wadanda suka afka cikin fatara da talauci sanadiyyar barkewar cutar, duk a kasashe masu tasowa su ke.

Cibiyar Goalkeepers 2020 ta ce bayan an shafe shekaru 20 cif ana samun raguwar fakiranci, yunwa da talauci a duniya, an a yanzu kuma cutar Korona ta maida hannun agogo baya.

“Annobar Korona ta haddasa wa kimanin mutum milyan 37 fatara da talaucin da dukkan su babu mai hanyar samun dalar Amurka 1.9 a kullum.

“Dama kuma gejin ma’aunin fatara da talauci shi ne a ce magidanci ba ya iya samun dala 1.9 a kullum. To fakiranci ya kai shi makurar bango kenan.

“Wanda ke da sana’a ko aikin da ke iya samun dala 3.20 a kullum, su ne masu dan karamin karfin a samu a kashe wajen cin abincin yau da gobe. Su ma din kusan mutum milyan 68 duk sun afka cikin fatara da talauci, matakin ‘yan ‘ya mu samu, ya mu sa bakin mu’. Haka dai rahoton ya bayyana.

Baya ga haddasa fakiranci, fatara da yunwa, rahoton ya ce annobar Korona ta haddasa yankewar abinci da kuma ruruta mace-macen kananan yara da mutuwar mata a wajen haihuwa.

Rahoton ya ci gaba da cewa karancin kudade da yankewar hanyoyin samu ga masu karamin karfi ya kara dagula al’amurra a kasashe masu tasowa.

An kuma buga misali da annobar farin-dango a Afrika ta Gabas, wadda ta rikita rayuwar milyoyin jama’a.

Rahoton ya ci gaba da kawo yadda cutar Korona ta yi illa a kasashe musamman a nan Afrika.

A Najeriya, idan ba a manta ba, cikin watan Agusta PREMIUM TIMES HAUSA ta buga wani rahoto da Hukumar NBS ta fitar cewa, kashi 27.1 na ‘yan Najeriya ba su da cin yau ko na gobe.

A cikin rahoton, Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta fitar da lissafin cewa akwai kashi 27.1 na yawan ‘yan Najeriya da ba su da aikin yin da za su rika samun kudin abincin yau ko na gobe.

Wannan kididdiga na nufin idan yawan jama’a a Najeriya sun kai milyan 200, to milyan 54,200 ba su da aikin yi kenan.

NBS ta ce wannan Kididdiga ta yawan adadin wadanda aka tababtar ne a watannin Aprilu, Mayu da Yuni na cikin 2020.

Rabon da NBS ta yi wannan kididdiga tun wadda ta yi cikin watannin Yuli, Agusta da Satumba na 2018, inda a lokacin aka samu kashi 23.1 na ‘yan Najeriya duk ba su da aikin yi.

Kafin wannan kuwa a lissafin watannin Oktoba, Nuwamba da Disamba, 2018, kashi 18.8 ba su da aikin yi.

Ya zuwa watanni ukun tsakiyar 2018 ne adadinya karu zuwa kashi 23.1, sai kuma yanzu cikin 2020 da adadin ya karu zuwa kashi har 27.1.

Annobar cutar Coronavirus ta zuzuta matsalar tabarbarewar tattalin arziki, inda manyan masana’antu suka rika sallamar ma’aikatan su, wasu kuma su ana zaftare musu albashi.

NBS ta ce yawan majiya karfin iya aikin neman kudi a Najeriya sun karu daga mutum milyan 111.1 cikin 2017 zuwa milyan 115.5 cikin tsakiyar 2018.

Sai dai kuma NBS ba ta fadi adadin yawan cima-zaunen da ke Najeriya ba, ballantana a san yawan su.

Share.

game da Author