Jam’iyyar PDP ta yi tir da ƙarin kuɗin mai da gwamnatin tarayya ta yi a ranar Laraba.
Kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya bayyana haka a madaddin jam’iyyar yana mai cewa tabbas akwai akwai rashin tausayi matuka a hakan da gwamnatin Buhari ta yi.
” Wannan karin kudin mai da gwamnati ta yi zai yi matuƙar sa kayan abinci da na masarufi su yi tashin gwauron zabi da talaka ne zai kwan ciki, dama kuma ya dandana kudar sa a karkashin wannan mulki na APC.
A ranar Laraba Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar ƙarin farashin litar man fetur zuwa naira 151.56 daga naira 138.
Hukumar Tantance Farashin Man Fetur (DPPRA) ce ta bayyana haka ranar Laraba a Abuja.
Baya ga ƙarin mai da aka yi kwatsam kuma da rana tsaka kawai kafin nan sai aka kara kudin wutan lantarki. Ba a gama samun natsuwa a kai ba aai ga shi kuma wai ankara kudin mai har zuwa sama da 150. Ina talaka zai sa kan sa.
” Duk da mun san cewa APC ba jam’iyya ce mai tausayin talaka ba, wannan ƙari da gwamnati ta yi babu tausayi a cikin sa ko shakka babu. Baya ga tsananin yanayi na rayuwa da mutane ke fama da shi a ƙasar nan ba a kyauta ba sake jibga musu sabbin jidali da aka yi ta hanyar kara farashin mai da wutan lantarki.
” Duk da cewa a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC ne aka wawushe naira Tiriliyan 14 da sunan biyan kuɗin tallafin mai da har yanzu gwamnatin bata fito ta bayyana matsayin ta game da wannan ƙorafi ba da kuma yin filla-filla da yadda aka kashe kuɗaɗen raran man fetur ɗin.
” Mu dai kiran mu ga mahukunta shine su shiga taitayin su domin tura ya kai bango, kada a dauka ƴan Najeriya basu san abinda suke yi ba, abin fa yanzu ya kai maƙura.
Discussion about this post