Kwamitin shirya zaben gwamnan jihar Edo na jam’iyya APC ta kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da hukumar Zabe ta bayyana, inda tace gwamnan jihar Godwin Obaseki da jam’iyyar sa ta PDP sun tafka magudi a zaben da akayi ranar Asabar.
Kwamitin shirya wannan zabe na jihar Edo karkashin Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce an tafka magudi da aringizo a wannan zabe da ya sa PDP ta yi nasara.
Sakamakon zaben da aka bayyana a garin Benin babban birnin jihar Edo, PDP ta samu Kuri’u 307,955, ita kuma APC ta samu kuri’u 223,619.
Kakakin kwamitin na APC John Mayaki ya ce jam’iyyar bata yarda sakamakon zaben ba cewa an tafka magudi.
” Jami’an tsaro sun kama mutanen mu babu gaira babu dalili sannan kuma a canja alkaluman zabe a wasu wurare da dama a jihar.
” PDP ta yi aringizon kuri’u a wasu wurare sannan an soke zaben wasu wararen da muke da karfi sosai. Bayan haka kuma sun rika canja alkaluman zaben ta hanyar kara wa dan takararsu kuri’un karya dana wofi.
A karshe yayi kira ga magoya bayan jam’iyyar cewa su kwantar da hankalin su, jam’iyyar na duba yadda abubuwa suka guda a lokacin zaben, nan da dan lokaci kadan za ta fitar da matsayinta.
Discussion about this post