OBASEKI: Goga, Kai Kadai Gayya

0

Dukan-kabarin-kishiyar da Gwamna Godwin Obaseki na PDP ya yi wa abokin karawar sa na APC, Ize-Iyamu, ta zama wata babbar ishara a siyasar Najeriya, musamman ma a zaben 2023 mai zuwa.

Obaseki ya zama raina kama ka ga gayya, saboda jarumtakar da ya nuna a matakai kusan 10 a zaben da aka bayyana shi ya yi nasara da ratar kuri’u masu dimbin yawa.

1. Obaseki ya kwace wa APC Jihar Edo, wadda ita kadai ce jihar Kudu maso Kudu da APC ta samu.

Jam’iyyar APC ta so lashe zaben Edo, ko ba komai dai ta samu ko da jiha daya ce a yankin da ke da arzikin danyen man fetur. Yanzu jihohin Kudu maso Kuku duk na PDP ne, kuma su ne aka fi dankara wa kudade a karshen wata, daga asusun Gwamnatin Tarayya.

2. Obaseki ya nuna za a iya kawo karshen siyasar ubangida a Najeriya. Ya kashe bakin Adams Oshiomhole tun daga sama har kasa.

3. Ya yi wa tsohon ubangidan sa Adams Oshiomhole mummunan kaye uku a jere. Kayen farko shi ne ya kulla masa tuggun da aka dakatar da shi a mazabar sa a cikin jam’iyyar APC, can a kauyen su.

Kaye na biyu kuma shi ne tsige Oshiomhole da aka yi daga shugabancin jam’iyyar APC, ta yin amfani da dakatarwar da shugaban APC na kauyen su ya yi masa.

Sai cikon kaye na uku shi ne Oshiomhole ya sa an hana shi tikitin tsayawa takara, ya fice daga APC, ya tsaya a PDP, kuma ya kayar da Oshiomhole da yaron sa Iyamu, wanda ya tsayar takara.

4. Obaseki ya ragargaza tuggun gogarman gidogar zabe, Gwamna Abdullahi Ganduje, wanda aka tura shugabancin kamfen din Ize-Iyamu.

5. Taron dangin da su Gwamna Yahaya Bello, Masari, El-Rufai da sauran gwamnoni su ka yi wa Obaseki, bai yi tasiri ba.

6. Obaseki ya lalata karfin siyasar Adams Oshiomhole a gida Edo da kuma Najeriya baki daya.

A Jihar Edo dai an kawo karshen sa. A Najeriya kuma a yanzu manyan APC za su kara tabbatar da cewa Oshiomhole ba alheri ba ne a jam’iyyar.

7. Karan-katsagallin da Oshiomhole ya rika yi a APC ya haifar wa jam’iyyar asarar jihohin Zamfara, Bayelsa, Oyo, Rivers da kuma Edo.

8. Darasin Da Obaseki Ya Koya Wa Buhari:

Shugaba Muhammdu Buhari ya yi sakaci da babban kuskure, ganin yadda ya na ji ya na gani APC ta hana Obaseki takara, saboda kawai ya ki yarda Oshiomhole ya juya shi.

Buhari ya yi sakacin da ya kyale Oshiomhole na ta yi wa APC giribtu a lokutan zabe, har abin na haifar musu asarar jihohi da dama.

9. Obaseki ya gagari Ganduje, wanda ake gani APC ta tura shi Edo ne domin ta kwace jihar daga hannun Obaseki, ko ana ha-maza-ha-mata.

10. Obaseki ya sacce tayoyin motar siyasar jagoran APC, Bola Tinubu, wanda ya rika kamfen kada a zabi Obaseki.

11. Nasarar Obaseki za ta sa APC ta shiga taitayin ta wajen kulla wa wasu tuggun hana su takara da kullatar su da talakawa suka yi

Share.

game da Author