Cibiyar Dakile Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar barkewar mummunar cutar Korona, wadda ta fi ta farkon nan da ake gaganiya da ita muni.
NCDC ta ce akwai yiwuwar sake barkewar cutar a Jihar Adamawa da wasu jihohin kasar nan. Ta ce cutar za ta iya sake dawowa ta addabi jama’a, musamman saboda yin biris da bin ka’idojin da jama’a ba su yi.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin Jami’i Mai Bada Shawara na Hukumar NCDC a Jihar Adamawa, Fahad Mohammed, a lokacin da ya ke jawabi ga taron wayar da kan jama’a kan cutar a Yola, Jihar Adamawa.
An shirya taron ne domin wayar da kan jami’an ‘yan sanda, ‘yan sintirin ‘Civil Defence, jami’a kula da shige da fice, jami’an Kula da Hadurra da na kula da jami’an kula da gidajen kurkuku.
Fahad ya ce NCDC ta tashi haikan domin ganin ana yi wa dimbin mutare gwajin Korona, yadda hakan zai sa a kakkabe cutar daga Najeriya.
Fahad ya ce “babbar damuwar mu a yanzu shi ne da mutane ba su zuwa ana yi masu gwaji. Saboda wasun su da dama ba su ma yi imani akwai cutar ba. Kuma rashin fitar su a yi masu gwaji ne ya kara sa ake samun karancin wadanda su ka kamu da cutar.
“Inda duk ake samun karancin masu kamuwa da cutar kwarona, to ba a yi wa mutane da dama gwaaji. Kuma wasu gwaje-gwajen idan an yi sai su ke nuna ba su dauke da cutar, to sai mu tambaye su, ya aka yi ba su dauke da ita? Kuma da wace sahihiyar na’ura aka yi masu gwajin?”
Jami’in dai ya nuna damuwar ganin yadda ba a samun masu cutar Korona a Adamawa, saboda ba a yin gwaji sosai.
“A Jihar Adamawa da akwai Kananan Hukumomi 7 da ba a taba zuwa aka yi wa mutum ko daya gwaji ba. Shin ku na nufin ku cewa babu mai dauke da cutar ko daya a wadannan kananan hukumomi bakwai kenan?
“A rika gargadi da jan hankalin jama’a su karfafa bin ka’idojin guje wa kamuwada cutar Korona, a rike rufe fuska da wanke hannaye da sabulun hana kawuwa da cututtuka da sauran matakan da su ka wajaba.”
Discussion about this post