Najeriya za ta kididdige yawan kamfanoni da adadin masu rajistar harkokin kasuwancin a kasa

0

Shekaru 22 kenan rabon da Najeriya ta kididdige yawan kamfanoni da adadin masu rajistar masana’antu da kasuwanci a kasar nan.

Amma Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta ce kwanan nan za ta fantsama gudanar da wannan kidaya a fadin kasar nan.

Kidayar mai suna ‘National Business Sample Census, rabon da a yi irin ta tun cikin 1998, kafin sojoji su mika mulki a hannun farar hula cikin 1999.

NBS ta ce za ta gudanar da aikin kidayar daga ranar 12 Ga Oktoba zuwa 12 Ga Disamba, cikin wannan shakara.

Bankin Duniya (World Bank) ne zai taimaka da tallafin kudaden aikin kididdigar.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Shugaban Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), Yemi Kale, wanda ya yi wannan sanarwa a ranar Litinin.

Ya kara da cewa irin wannan kididdigar kamata ya yi a ce ana yin ta duk bayan shekaru 10.

“Manufar wannan kidaya ita ce a kirkiro wata alkibla ga kamfanoni, cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da masana’antu ta yadda za su jibinci irin harkokin kasuwancin da kowane bangare ke samarwa a cikin al’umma.

Sannan kuma ana so a fito da wani matsayi da mataki na cancanta da nagartar masana’antu, kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da cinikayya a Najeriya.

Sauran manifofin sun hada da a san yawan cibiyoyin, yawan kamfanonin da kuma yawan adadin masana’antun baki daya.

Karin dalilin kuma shi ne domin Najeriya ta samu gsmsasshen bayanin irin fasalin tattalin arzikin kasar dungurigum.

Kakakin Yada Labarai na Hukumar NBS, Ichei Joel ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Shugaban Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), a Abuja.

Kididdigar za ta gudana a fadin jihohin kasar nan 36 da Abuja. Kuma za a yi a dukkan bangarorin harkokin kasuwanci.

Share.

game da Author