Hukumar kula da Ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta bayyana cewa Najeriya hada magunguna akalla kashi 60 bisa 100 na wadanda aka fi amfani da su a kasar nan.
Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta fadi haka a taron tattauna rage yawan dogaro da kasashen waje da a ke yi wajen shigowa da magunguna.
Mojisola ta ce fara hada magunguna a kasar na zai inganta tattalin arzikin kasar sannan da rage yawan dogaro da kasashen waje.
Idan ba a manta ba a shekarar 2019 ne Hukumar NAFDAC ta ce tana kokarin farfado da kamfanonin sarrafa magungunan dake kasar nan domin samun daman sarrafa kashi 60 bisa 100 na magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje.
Adeyeye ta ce farfado da kamfanonin zai taimaka wajen hana shigo da jabun magunguna wanda suka karade kasar nan yanzu.
“ Wani abin tashin hankali da hukumar NAFDAC ke fama da shi shine jabun magunguna wanda ke neman ya mamaye kasuwanin kasar nan.
“ Mun gano cewa wasu daga cikin jabun magungunan da ake shigo dasu suna dauke da shaidar rajistar hukumar NAFDAC wanda tun daga can ake lafta musu tambarin mu, wasu kuma tsuran su aka shigowa da su.
Adeyeye ta kuma ce hukumar ta inganta hanyoyin inganta magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje musamman wadanda ake shigo da su daga kasashen Chana da Indiya.
“Kafin a loda magungunan a jirgi zuwa kasar nan sai mun duba su tatas sannan bayan sun iso Najeriya kuma za mu sake duba su da yin gwajin su.
Discussion about this post