Najeriya ta tasa ƙeyar Misirawa 10, Bafaranshe da wasu baƙin-haure zuwa kasashen su

0

Gwamnatin Najeriya baki ‘yan kasashen waje 19 daga kasar nan zuwa kasashen su.

Kakakin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Sunday James ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya turo wa PREMIUM TIMES a ranar Juma’a.

Cikin sanarwar dai an nuna cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sa hannun fatattakar su zuwa kasashen na su.

Wannan umarni ya na bisa ka’idar Doka ta Sashe na 45 da ke Karamin Sashe na (1) da kuma Sashe na 47 da ke Karamin Sashe na (1) na Dokar Shige-da-fice Ta Kasa ta 2015.

Daya daga cikin wadanda aka kora mai suna Ali Mahamat an kira shi zuwa kasar Faransa, yayin da wani mai suna Kasinayhan Ramasamy, an tankada keyar sa zuwa Indiya.

Sanarwar ta kara da cewa an samu Mahamed da laifin jefa kan cikin muggan laifukan da ka iya haifar da matsalar tsaro da dngantaka tsakanin Najeriya da wata kasa makauciyar ta a Barno jihar.

Shi kuma Ramasamy an samu ya na aikin tsaron shago a Kano.

Sanarwar ta kara da cewa akwai kuma wasu Misirawa su 10 da su ka karya ka’idoji da sharuddan da dokokin shigowa Najeriya. Su ma an kora su zuwa kasar Masar da iznin Minista Aragbesola.

Sai kuma wasu ‘yan Srilanka su bakwai da aka daure a kurkuku, saboda an kama su day laifin da ya shafi satar danyen man fetur. Su ma kotu ta bada umarnin a tasa keyar su zuwa kasar su.

Kwanturolan NIS, Muhammad Babandede ya umarci cewa duk wani bakon da zai shigo Najeriya, to ya tabbata ya bi doka kuma ya kiyaye dukkan ka’idojin zama Najeriya.

Share.

game da Author