Najeriya ta kafa kwamitin magance cutar Korona da magungunan gargajiya

0

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya kaddamar da Kwamitin Magance Cutar Korona Da Magungunan Gargajiya, domin gano hanyar rabuwa da cutar ta dabarun amfani da magungunan gargajiya da za a rika harhadawa a nan cikin gida.

Cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha, Abdulganiyu Aminu ya fitar a ranar Litinin, ya ce Minista Onu ya yi gargadin cewa har yanzu annobar Korona na yi wa harkokin lafiya da tattalin arzikin kasar nan babbar barazana.

Dalili kenan ya ce akwai gaggawar bukatar a zabura wajen gano dabaru da fasahar amfani da magungunan gargajiya na nan cikin gida domin a yi wa Korona kwaf-daya.

Kwamitin inji Minista, an kafa shi ne tare da dora masa alhakin tantance ikirari da magungunan da wasu likitoci ko masu harhaɗa magungunan zamani da na gargajiya suka yi cewa sun gano maganin warkas da cutar Korona.

Minista ya umarci mambobin kwamitin, wadanda suka hada hada manyan likitoci su yi aiki tukuru wajen tantance ainihin gaskiya da kuma sahihin garantin kowane magani da aka yi Ikirarin zai iya warkas da cutar Korona.

“Ina da yakini cewa idan aka samu maganin warkas da cutar Korona a Najeriya, to martaba da kimar kasar nan ta za karu, daukakar ta ma za ta karu a duniya.” Inji Minista Onu.

Sannan kuma ya ce martabar masana kimiyya na kasar nan za ta karu a duniya, kuma Najeriya za ta samu kudin shiga ta fuskar kimiyya.

Shugaban Kwamitin kuma Shugaban Kungiyar Masana Kimiyya ta Kasa, Motso Onuoha, ya ce Najeriya na da karfin da za ta iya samar wa kan ta mafita wajen kawar da cutar Korona, ta hanyar kirkiro magunguna a cikin gida.

Share.

game da Author