“Najeriya na bukatar a dukufa da yin addu’o’i domin hana kasar tarwatsewa, sakamakon rarrabuwar da ke addabar kasar.”
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi wannan kakkausan furuci yayin da ya ke jawabi a Hedikwatar Babban Coci na Kasa da ke Abuja, a ranar Lahadi, domin yin addu’o’in cikar Najeriya shekaru 60 bayan samun ‘yanci.
“Sai dai inda Allah ya taimake mu, har yanzu bangon da mu ke jingine bai fadi kasa ba. Amma fa tabbas wannan bango ya tsatstsage, tsagar da ka iya sa ya zube kasa, Najeriya ta rarrabu.”
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci Osinbajo, kuma shi ne ya karanta jawabin sa a madadin sa.
Ya ce akwai bukatar a yi da gaske s hada hannu da karfi a tallabe wannan bango domin a hana shi zubewa kasa.
Yayin da ya ce ya na da yakinin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci zai iya sake farfado da Najeriya, Osinbajo ya jaddada cewa malaman addinai ne a wannan lokacin su ka ci cancanta su fi bada karfi wajen yin addu’o’i.
Shi kuwa Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa, Samson Atokunle, ya yi kira ga shugabannin su rika jaddada adalci, wanda ya ce tabbas sai da adalci sannan zaman lafiya da kaunar juna ke wanzuwa da dawwama a cikin kasa.
Osinbajo ya yi wannan kakkausan kalami makonni kadan bayan da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya ta kamo gargarar rugujewa.
Discussion about this post