Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta gargaddi ma’aikatan kiwon lafiya da su nisanta kansu daga fifita amfani da madaran gwangwanin fiye da nonon uwa.
Gwamnati ta ce za ta dauki mummunar mataki akan duk ma’aikacin lafiyan da ta kama yana haka a asibitocin dake jihar.
Shugaban hukumar Nantim Mullah ya sanar da haka a taron tattauna mahimmancin shayar da jarirai nonon uwa da aka yi a garin Kaduna a makon da ta gabata.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne majalisar Kasa ta Kara duba dokar inshoran lafiya na kasa domin saka mata masu shayar da jarirai nonon a cikin shirin.
Majalisar ta ce yin haka zai taimaka wajen wayar da kan mata da sanin muhimmancin shayar da jariran su nonon domin inganta lafiyar su a kasar nan.
Shugaban kwamitin kiwon lafiya na majalisar Ibrahim Oloriegbe ya sanar da haka a taron tunawa da mahimmancin shayar da jarirai nonon uwa da kungiyar ‘Save the Children International’ ta yi a Abuja.
Mahimmancin shayar da jariri nonon uwa
Likitoci sun bayyana shayar da jariri nono zalla musamman na tsawon watanni shida ko Kuma fiye da abu ne da ke kara lafiyar jarirai.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya fadi haka, sannan ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara mace-macen yara da mata.
” Shayar da yaro ruwan nono zalla na tsawon watanni shida hanya ce dake taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro da na uwa.” Inji Thompson.