A ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na ganin an kawo karshen ayyukan ta’addanci da hare-hare a jihar Katsina, Rundunar Ƴan sandan jihar ta cafke masu aikata laifuka da dama a jihar.
Waɗanda aka kama sun haɗa da waɗanda ake zargi da aikata fyade 140, Ƴan Bindiga 50, sannan kuma jami’anta sun kwato shanu sama da 2O0, motoci biyu da babura 20.
Wannan yana daga cikin ayyukan da rundunar tayi a karo na biyu.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Sanusi Buba, ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a , a Katsina.
Ya ƙara da cewa an samu nasarar kama waɗannan ɓata gari ne ta hanyar
tattara bayanan sirri.
“ Baya ga kamen da muka yi an kwato bindigogi kirar AK 47 guda tara, bindigogi 20 kirar hannu, motocin hawa biyu, da babura 20, da shanu 220 da suka salwanta, da kuma kudi Naira N685,000.
“ Bayan haka jami’an tsaro sun kashe‘ ƴan bindiga 15 sannan ta kuƙutar da mutum 2 da aka yi garkuwa da su.
” Haka kuma an damke mutane 140 da ake zargi da aikata fyade kuma dukkansu an gurfanar da su a gaban kotu a jihar.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa da hare-haren ƴan ta’adda yayi ƙamari.
Jihohin Kaduna da Zamfara ma na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴan ta’adda.
Discussion about this post