Kungiyar Kare Muradin Harkokin Musulmi, wato MURIC, ta nemi a gaggauta kafa kotunan musamman wadanda za su rika hukunta laifukan satar kuɗaɗen gwamnati.
Shugaban Kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya sanar da haka, a cikin wata takarda da ya fitar wa manema labarai.
Akintola ya ce duk da gwamnatin Buhari na ƙoƙarin ta wajen ganin an daƙile rashawa da cin hanci, amma kuma akwai tulin shari’un da ake ta kwan-gaba-kwan-baya a kan su, kuma ba a san ranar kammala su ba.
Ya ce kafa kotunan zai sauƙaƙa cinkoso, daɗewa da da mantawa da ake yi da shari’un waɗanda suka sace dukiyar jama’a.
” Ƙiri-ƙiri mutane da dama an san ɓarayi ne, idan aka kai su kotu, sai su yi amfani da wasu hukunce-hukuncen shari’a-saɓanin-hankali yadda shari’ar za ta yi tsaye cak, ta kakare. Sai a daɗe har su bar duniya ba a kammala shari’ar ba.
A Gina Wa Barayin Gwamnati Kurkukn Su Daban:
“Saboda bahaguwar shari’ar da ake yi a karkashin tsarin mulki, sai ka ga manyan mutanen da kamata ya yi su na kurkuku a ɗaure, amma sai ka ga su na walwala a cikin jama’a babu kunya.
“Ya kamata a riƙa ɗaure su a kurkuku na su daban. Satar kuɗin al’umma ba karamar illa ba ce ga kasa.
“Manyan marasa tausayi kuma su ne masu satar kuɗaɗen tsoffin ƴan fansho. Su waɗannan kamata ya yi a kurkuku ɗin ma a riƙa ɗaure su da sarƙa a hannu da kafa awa 24 babu kwancewa a kowace rana. Rashin tausayin na su ya yi yawa.
Masu Fyaɗe: “Waɗannan ba su da wani amfani a cikin al’umma. Ya kamata a riƙa kashe masu mazakuta, ta hanyar daddaƙe masu golaye, su daina sha’awar mace har abada.”
Akintola ya roƙi ƴan Majalisar Dattawa su hanzarta kafa dokar kafa kotunan na shari’ar barayin gwamnati, domin aikin da hakkin duk a kan su ya ke.