MUHAWARAR TRUMP DA BIDEN: Yadda ƴan takarar shugabancin Amurka su ka riƙa ɗura wa juna cin mutunci a gaban jama’a

0

Muhawarar da ƴan takarar shugabancin Amurka Donald Trump da Joe Biden su ka yi a bainar jama’a, ta yi zafin da dattawan biyu su ka shafe mintina 90 su ka ɗura wa juna ƙalamai na rashin mutunci.

Trump wanda ke wakiltar jam’iyyar Republican, shi ke kan mulki, kuma ya na neman a sake zaben sa ne a zabe mai zuwa.

Shi kuwa Biden, ya na wakiltar jam’iyyar Democrat, kuma ya taba yin Mataimakin Shugaban Amurka.

Wannan ce mahawara da farko da ƴan takarar biyu su ka kafsa muhawara, wadda fitaccen dan jaridan na na Fox News, Chris Wallace ne mai shiga tsakanin ‘yan takarar biyu.

Daga cikin batutuwan da su ka tattauna akai sun hada da ɓarkewar cutar Coronavirus, wadda ta kashe sama da Amurkawa 200,000.

Sai kuma batun haraji, muggan laifuka, tattalin arziki, dumamar yanayi, zaben shugaban kasa mai zuwa da kuma wasu muhimman batutuwa.

Cin Mutunci Da Wulakanta Junan Su:

“Kai tafi, ka rufe wa mutane wannan kazamin bakin na ka. Ka na magana irin ta ‘yan gada-gada, kamar ba Shugaban Kasa ba.” Haka Biden ya shaida wa Trump a lokacin da ya ga ya na shisshige masa hanci da kudundune.

Trump ya ƙaryata ya rama raddi,sai dai kuma ya rika wuce-gona-da-iri wajen katsalandan idan mai shiga tsakani ya ba Biden fili ya yi magana.

Wallace ya nemi Trump ya daina saka baki idan Biden na magana, amma maimakon Trump ya rufe bakin sa, sai cewa ya yi, “to ai ban ga wani abin arziki da zai iya fitowa daga bakin mai birkitattar kwakwalwa ba.”

Trump bai haƙura ba, ya sake kwankwatsar Biden, ana cewa ya yi shiru, amma ya ki.

“Ka na ta kame-kamen sunan kwalejin da ka yi. Tun da ku ka ga haka, to ko dai a kwalejin banza ka yi karatu, ko kuma a ajin ku kai ne dan banzan da ke zuwa na karshe idan an yi jarabawa a aji.”

Share.

game da Author