Makonni biyu bayan sanarwar cewa Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Jihar Adamawa, Stephen Mamza ya kamu da cutar Coronavirus, an bayyana warkewar sa har ma an sallame shi daga cibiyar killace masu fama da cutar.
A wani taro da manema labarai da ya yi a Yola, Mamza wanda kuma shi ne Babban Limamin Darikar Katolika na Adamawa, ya gode wa Allah da sauran jama’a da kuma jami’an kiwon lafiya da suka rika kula da shi.
Sai dai kuma ya bayyana cewa cutar Coronavirus ba abin tayar da hankali ba ce. Kawai dai ana firgita mutane, a na kara zuzuta ta fiye da yadda ta ke.
“Ni ina ganin kawai ana zuzuta cutar Coronavirus ce ana firgita mutane, har su rika tayar da hankalin su, su mutu saboda tsoro da fargabar cutar Coronavirus.
“Da an ce mutum ya kamu da cutar Coronavirus, shi da kan sa ke sallamawa da duniya, ya ji kamar hukuncin kisa ne aka yanke masa. Sai ya tashi hankalin sa, barci ma ya gagare shi. Ita kuma mutuwa, sai ta bi ta danne kawai.” Inji Mamza, wanda babban Bishop ne.
“Mutum zai iya kamuwa da cutar har ya warke amma bai ma san ya kamu ba, kuma babu wata alama a jikin sa. Saboda cutar mataki-mataki ce. Amma da mutum ya kamu aka sanar da shi, to sai ya ji kamar kofar tafiya lahira ce aka bude aka ce ya shiga ya tafi.
Cutar Korona ta kashe kusan mutum milyan daya a duniya. Ta kama sama da mutum 50,000 a Najeriya, ta kashe sama da mutum 1,000.