Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewabusa taba sigari na daya daga cikin abubuwan dake haddasa cututtukan dake kama zuciya da haka ke kashe akalla mutum miliyan 1.9 duk shekara.
Binciken ya kuma nuna cewa shakar hayakin taba a dalilin zama tare da masu busa ta na yin sanadiyyar rayukan akalla mutum 200,000 duk shekara.
WHO ta kebe ranar 29 ga watan Satumba domin wayar da kan mutane game da illar dake tattare da busa taba sigari.
Saka dokar hana siyar da Taba Sigari a Najeriya
Idan ba a manta ba a 2015 gwamnatin Najeriya ta kafa dokar hana siyar da taba sigari musamman ga matasa ‘yan kasa da shekara 18.
Dokar ta kuma hana matasa irin haka yin tallar sigarin da tallata sa a gidajen talabijin da radiyon kasar nan.
Gwamnati ta yi haka ne saboda sakamakon biniciken da ya nuna cewa kashi 15.4 bisa 100 na mutanen Najeriya (Maza da mata) na busa taba sigari sannan kashi 89 bisa 100 na matasa ‘yan shekara 18 ne suka fi siyan ta, wato amfani da ita.
Sakamakon binciken ya nuna cewa babban birnin tarayya Abuja ta fi yin kaurin suna wajen yawan masu busa taba sannan jihohin Ekiti, Katsina da Edo.