MASANA KIMIYYA: Za mu tabbatar maganin Korona da za a fitar ya tsallake gwajin tabbatar da ingancin sa

0

Masana kimiya dake aiki da kamfanonin sarrafa magunguna guda Tara sun yi alkawarin hadawa da samar da maganin rigakafin cutar korona da suka tabbatar da inganci da sahihancin sa.

Wadannan kamfanoni guda tara sun hada da AstraZeneca, BioNTech, GlaxoSmithKline, Johnson & Johnson, Merck, Moderna, Novavax, Pfizer da Sanofi.

Kamfanonin sun ce yanzu da duniya ta matsu a samar da maganin rigakafin cutar korona sun ce za su fitwr da maganin rigakafin ne bayan sun gudanar da gwaje-gwaje bisa ga sharuddan kimiya domin ganin maganin bai cutar da kiwon lafiyar mutane ba.

Idan ba a manta ba a watan Agusta ne Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa masana magunguna a kasar sun kammala hada rigakafin Korona da kowa zai yi amfani da shi.

Masana kimiyar dake hukumar gudanar da bincike ‘Gamaleya Institute’ dake Moscow ne suka hada wannan magani na rigakafi bayan akalla watanni watanni biyu suka yi suna gwajin inganci da sahihancin sa.

Sannan kuma ranar Juma’ar da ta gabata ne kasar Rasha ta gabatar da samfurin maganin rigakafin cutar korona wa ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare a Abuja.

Ehinare ya ce za a aika da wannan magani ma’aikatar NAFDAC da sauran hukumomi gudanar da bincike Kan magunguna dake kasar nan domin cigaba da aiki a kai.

Kasar Afrika bayan ta karbi samfarin maganin ta yi Kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da sahihancin maganin kafin a fara amfani da shi.

Share.

game da Author