MAKON KURAME: Ba za mu bar nakasassu a baya wajen inganta rayuwar al’umma ba -Minista Sadiya

0

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta ci gaba da mara wa dukkan nakasassu da kurame baya don a saka su cikin duk wani shiri, a kare hakkin su kuma a ba su damar shiga dukkan al’amurran cigaban al’umma.

Hajiya Sadiya ta yi wannan maganar ne a Abuja a ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2020 a wajen bikin zagayowar Makon Kurame na Duniya da kuma Ranar Magana Da Hannu ta Duniya.

Ta kara da cewa ma’aikatar ta ta kasance kan-gaba wajen ganin an kafa Hukumar Kula da Nakasassu ta Kasa don tallafa wa muradun dukkan mutanen da ke fama da wata nakasa a Nijeriya.

Ta ce: “Daya daga cikin dalilan ware Ranar Magana Da Hannu ta Duniya shi ne domin a habaka yanayin maganar da kuma al’adun kurame a dukkan fadin duniya.

“Ina tabbatar maku da cewa Gwamnatin Tarayya, ta hanyar wannan ma’aikata, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kula da dukkan mutane masu wata nakasa a Nijeriya a harkar gudanar da mulki ta hanyar kawar da duk wani tarnaki wanda kafin yanzu ya zame masu karfen ƙaka a wajen cigaban su.”

Tun da farko, sai da Sakatare-Janar na Babbar Kungiyar Kurame ta Nijeriya, Chidi Topaz Oluije, ya gode wa ministar saboda yadda ta aiwatar da Ranar Kuramen a Nijeriya domin kuwa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akwai kimanin mutum miliyan goma da ke fama da kurunta a Nijeriya.

Ya ce: “A cewar WHO, akwai kurame miliyan goma a Nijeriya. Wannan ya nuna cewar Magana da Hannu babban muhimmin abu ne a gare mu wajen samun damar cudanyar duniyar kurame da ta masu ji tare da shiga cikin harkokin siyasa, kiwon lafiya da duk wani sashe na ƙasar nan.”

Bikin dai ya samo asali ne daga Kudiri mai lamba A/RES/72/161 na Majalisar Dinkin Duniya wanda aka rattaba a cikin 2017 kuma aka ware ranar 23 ga Satumba ta kowace shekara a matsayin Ranar Magana da Hannu ta Duniya.

Jigon ranar ta bana dai shi ne ‘Jaddada Hakkin Dan’adam na Kurame’ (wato a Turance ‘Reaffirming Deaf People’s Human Rights’).

Dukkan masu ruwa da tsaki a wannan al’amari za su ci gaba da ayyukan bikin daga ranar 26 zuwa 30 ga Satumba, 2020 a birnin Kano.

Share.

game da Author