Asusun Kula da Yara Kanana Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta ce ta tallafa wa kananan yara sama da milyan daya a cikin shekara daya, a yankin Arewa maso Gabas, domin ganin sun samun ingantacce kuma nagartaccen ilmi.
UNICEF ta ce yaran wadanda ta taimakawa a Arewa maso Gabas din, duk wadanda ba su day hali ko sukunin samun zuwa makaranta ne.
Ta ce ta na tabbatar da ganin cewa an sama musu wurin samun ilmi a cikin muhallai masu matakan tsaro.
Jami’ar Kula da Ilmi ta UNICEF a wuraren masu gudun hijira, Judith Giwa Amu ce ta bayyana haka a manema labarai a Abuja, cikin wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a Abuja.
Ta ce UNICEF ta hada guiwa da wasu bangarori inda ta shige gaba wajen tabbatar da samar da yanayi mai kyau, musamman ga yara masu gudun hijira da wadanda rikice-rikice ya kassara yankin su, domin su samu ilmin da zai ceci rayuwar su nan gaba.
Hakan a cewar ta zau kuma kara nesanta su daga kwadayin shiga kungiyoyin ta’addanci.
Giwa-Amu ta ce tun da farko UNICEF ta kudiri aniyar tallafa wa yara milyan 1.5 ne, amma dai guda milyan daya ne suka samu katarin amfana da shirin.
Ta ce a Jihar Benuwai ma UNICEF ta tallafa wa kananan yara 11,000 daga cikin 12,000 da ta kudiri aniyar tallafawa a fannin inganta ilmi a wuraren da ke da zaman lafiya.
Ta ce yaran da aka tallafawa din duk a yankunan da rikici ya yi wa katutu.
“Mu na wannan kokarin ne, saboda mun san cewa ilmi shi ne babban ginshiki kuma makamin kare kai daga afkawa wata mummunar hanyar da a karshe yaro zai yi da-na-sani, idan ya afka.
“Kuma hanya ce ta ceton rayuwa, saboda idan yaro ya maida hankalin sa ga karatu, to sun daina gararamba a kan titi kenan, ballantana har wasu batagari su cusa musu mummunar akidar da za a maida su batagari ko a sace su a yi garkuwa da su.”
Discussion about this post