Yadda Mahara suka kashe jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa FRSC biyu suka arce da wasu 10

0

Mahara dauke da bindigogi sun farwa jami’an hukumar kiyaye hadura ta Kasa a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Sokoto da Kebbi.

Jami’an su 26 sun taso zuwa makarantar koyan sanin makaman aiki na hukumar dake Udi, Abuja a cikin manyan motoci biyu kirar bus, kamar yadda kakakin hukuma ya fadi a wata takarda da hukumar ta fitar ranar Litini.

Maharan sun tare waɗannan jami’ai ne a mahaɗar Mararraban Udege, dake jihar Nasarawa da misalin karfe 8 na safe.

Kazeem ya bayyana cewa jami’i daya ya mutu nan take sannan Jami’ai Takwas sun tsira babu ko rauni, sauran 10 kuma maharan sun yi awan gaba da su.

Kazeem ya kara da cewa shugaban hukumar, Boboye Adeyemi ya ce tuni dai har an fara bincike akai da kuma shirin fantsama daji domin kuɓutar da waɗanda aka sace da kamo waɗannan mahara.

Sannan ya yi kira ga sauran ma’aikata da su cigaba da aiki tukuru, kada su bari wannan abu da ya faru ya tada musu da hankali.

Ya ce hukumar zata yi aiki da sauran hukumomin tsaro domin fallasa waɗanda suka aikata wannan mummunar abu da kuma hukunta su, bayan an kuɓutar da waɗanda aka waske da su.

Idan ba a manta ba an kai irin wannan hari a Tungan Maje dake Abuja, inda aka waske da mutane sama da 10 a makon da ta gabata.

Har yanzu ba a ba da sanarwar ceto su ba.

Share.

game da Author