MA’AIKATAN BOGI: An gano Ƙananan Hukumomi 19 na satar naira bilyan 1.8 a duk shekara a Barno

0

Jami’an Ƙananan Hukumomi 19 a Jihar Barno sun kwashe shekaru su na satar kuɗaɗen jIhar har naira bilyan 1.8 a duk shekara, ta hanyar biyan albashi ga ma’aikatan bogi na tsawon shekara goma.

Barno ce jihar da ta fi sauran jihohin Arewa maso Gabas fama da Boko Haram, ‘yan ta’addar da su ka kashe sama da mutum 40,000 tun daga 2009. Wasu milyoyi kuma sun rasa gidajen su.

Dalla-dallar kididdigar yadda aka rika satar kudaden na cikin wani rahoto da Kwamitin Tantance Albashi ya mika, wanda Gwamnatin Jihar Barno ta kafa.

Wakilin PREMIUM TIMES ya ga kwafen rahoton, wanda aka damka wa Gwamna Babagana Zulum.

A cikin rahoton, kwamitin ya ce ya kammala binciken kananan hukumomi 19 daga cikin 27 din da ke Jihar Barno.

Kwamitin ya ce a cikin watan Yuni ya karɓo naira milyan 150, albashin da har yau masu karɓa ba su je sun karɓi kuɗaɗen ba.

Kwamitin ya ce an samu kudaden bayan da Kwamiti ya jajirce cewa kowane mai karbar albashi ya bayyana a gaban kwamitin tare da takardun sa, domin a tantance matsayin sa a inda ya ke aiki.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Barno, Sugun Mai-Mele ya tabbatar da lamarin a tattaunawar da ya yi da PREMIUM TIMES.

“Wadannan naira milyan 150 da aka gano duk wata ana sacewa a Kananan Hukumomi 19, sun nuna ana satar naira bilyan 1.8 kenan duk shekara.

“Ka ga kudin da su ke sacewa sun kai adadin naira bilyan 1.8 da Barno ta ware wajen ayyukan samar da ruwan sha cikin shekarar 2012 a dukkan kananan hukumomin jihar Barno su 27.

A Jihar Barno an kasa aiwatar da biyan tsohon mafi kankantar albashi na naira 18,500. Ba ma ta batun sabon mafi kankanta naira 30,000 ake yi ba. Hakan ya faru ne saboda gwamnatin jihar ta ce babu isassun kudade.

Amma kuma kididdiga ta nuna za a iya biyan ma’aikata 8,108 naira 18,500 na mafi kankantar albashi da naira bilyan 1.8 har tsawon watanni 12 cur.

Jami’ai a Ma’aikatar Kananan Hukumomi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu biyan albashi a kananan hukumomin 19 su na karbar kudaden albashin da sun fi karfin yawan sahihan ma’aikatan su, fiye da shekara goma kenan.

Kenan hakan na nufin kananan hukumomin 19 sun karbi naira bilyan 18 da sunan biyan albashi, amma duk ma’aikatan bogi ake biya, wanda babu su, sai dai sunayen su kawai tsawon shekara goma.

Wannan tantancewa da ta kai ga fallasa wannan harkalla dai, gwamnatin Barno ce tw shigo da tsarin a jihar, domin dakile rashawa da wawurar kudade a Kananan Hukumomi.

Kwamitin Bincike dai bai kammala da sauran kananan hukumomi 8 ba tukunna. Don haka ba a san ko nawa za a fallasa an rika saa tsawon shekara 10 a sauran kananan hukumomin ba.

Yadda Aka Fallasa Ma’aikatan Boge:

Kwamishinan Kananan Hukumomi ya ce umarni kwamiti ya bayar cewa kowa ya je ya karbi fam ya cika domin a tantance shi.

“To da yawan wadanda suka karbi fam din, sun sulale ba su koma gaban kwamiti ba. Wasu kuma sun cike fam din sun mayar, amma ba su gabatar da kan su wurin tantancewa a gaban kwamiti ba.”

“Watanni uku aka ba su wa’adin karbar fam su cike su maido, amma har yau babu su ba labarin su.

“Da watan Yuni ya zo aka biya albashi, sai ga rarar naira milyan 150 an samu a kananan hukumomi 19. Kuma tun daga ranar da aka biya albashin har zuwa yau, babu wanda ya kawo koken cewa ba a biya shi albashin sa ba.”

Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar Barno ta ce ba ta da wata matsala da aikin tantancewa da kwamitin ke yi.

Shugaban Kungiyar ta NULGE, ta Jihar Barno, Mustapha Bulama, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa matsawar dai ana aikin ne domin a tsaftace tsarin biyan albashi, ta hanyar toshe hanyoyin satar kudade, to su na goyon bayan shirin.

Share.

game da Author