Kwanaki 14 da sace yaran makaranta a Kaduna, gwamnati bata ce komai akai ba

0

Idan ba a manta a watan Agusta ne wasu mahara akan babura dauke da bindigogi suka afka wani makarantar sakandare mai suna ‘Prince Academy’ a daidai dalibai na daukan darasi a ajujuwansu a karamar hukumar Chikum, dake jihar Kaduna.

Maharan sun tarwatsa dalibai da malamansu, suka sace wasu daga cikin daliban bakwai da malamar su daya.

Yanzu kwanaki 14 kenan da aka arce da dalibai 7 da malama daya daga wannan makaranta kuma gwamnatin tarayya, jiha da karamar hukuma ba su ce komai akai har yanzu tunda aka yi garkuwa da wadannan yaran makaranta.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin samun karin bayani daga mahukuntan jihar amma hakan bai yiwu ba domin babu wanda ya ce komai akai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Muhammed Jalige bai daga wayar sallular sa ba da aka kira shi amma kwamishinan ‘yan sanda Muri Musa ya ce kakakin zai Yi magana da wakiliyar da zaran ya samu lokaci.

Jihar Kaduna kamar wasu jihohin Arewa Maso Yamma na fama da matsalar yan ta’adda. Wannan ba shine karon farko ba da ake kai samame makaranta a jihar.

Wannan karon gwamnati bata ce komai akai ba tun bayan da abin ya auku.

Share.

game da Author