KURUNKUS: Zan cigaba da murza tamola a Barcelona – Inji Messi

0

Fitattacen ɗanwasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona Leo Messi ya bayyana cewa ya hakura zai cigaba da murza tamola a ƙungiyar har sai kakar wasa mai zuwa.

Messi ya bayyana haka ne a hira da yayi da jaridar Goal.com ranar Juma’a.

Messi ya ce iyalan sa na daga cikin waɗanda suka sa ya canja shawara.

” Ko da na gaya wa matata da ƴaƴana cewa zan bar Barcelona sai suka barke da kuka kamar an yi mutuwa, matata tace na yi hakuri, sannan ƴaƴana suka ce sun saba da Barcelona ba su so su koma wata kasar yanzu, sannan ga kuma saboda makaranta a nan Barcelona din.

Daga nan sai Messi ya ce ya hakura da barin kulob din zai cigaba da wasa. Sai da kuma ya bayyana takaicin sa bisa abinda ya ce rashin cika alkawari daga shugaban Kulob din Bautomeu.

” Alkawarin da muka yi da Kulob din tun farko shine duk lokacin da naga dama zan iya yin sallama da Kulob din amma kuma sai yanzu Bautomeu ya yi ikirarin wai zan biya Kulob din Euro miliyan 700 idan na matsa sai na tafi.

” A wannan lokaci muna kokarin kammala wasan lik, sannan kuma kowa ya san yadda annobar Korona ta canja komai musamman a wasan kwallon kafa.

” Karshe dai sai dai in je Kotu da kungiyar wanda ni ba zan taba yin haka ba domin kungiyar ta yi min rana, kuma nima na yi mata rana. Ba zan iya shiga kotu da Barcelona ba.

Share.

game da Author