KUƊI MAI SA FAƊA DA UBA: Gwamnonin Jihohi 36 sun maka Buhari kotu

0

Jihohin Tarayya Najeriya 36 sun garzaya kotu sun gurfanar da Shugaba Muhammadu Buhari, inda su ka roƙi Kotun Ƙoli ta dakatar da shugaban aiki da Dokar Musamman da ya ƙirƙiro, wacce ta bai wa kotunan jihohi cin gashin kai.

Buhari ya sa wa Dokar Musamman mai lamba 00-10 ta 2020 hannu, wadda ta bai wa ɓangaren shari’a na jihohi ikon ƙarɓar kuɗaɗen su kai-tsaye daga Gwamnatin Tarayya, ba tare da sai an tura wa jihohi sannan su ba su ba.

A cikin ƙarar da su ka maka Buhari a kotu, sun yi ƙorafin cewa dokar na ƙoƙarin ɗora masu nauyin biyan Kotunan Jiha, Kotunan Daukaka Karar Shari’ar Musulunci da Kotunan Daukaka Karar Shari’un Gargajiya.

Karar dai gagarima ce, kuma Gwamnatocin Jihohi sun dauke ta da muhimmanci, domin sun dauki Gaggan Lauyoyi 9, duk ‘SAN’. Sun kara rakito wasu lauyoyin shida domin su taimaka musu kokawar kayar da Buhari a Kotun Tarayya.

Tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Augustine Alegeh ne jagoran lauyoyin da za su fafata da Buhari a Kotun Koli.

Alegeh ya ce abin da Buhari ya yi haram ne, ya karya doka, domin ya dauke nauyin kashe wa kotunan kudade daga Tarayya zuwa wuyan Jihohi.

Sun ce gangancin da Buhari ya yi a matsayin sa na shugaban kasa, ya kauce wa Sashe na 6 da na 8 (3) na Kundin Tsarin Dokokin Najeriya na 1999.

Sun ce wannan sashe na doka ya dora nauyin ciyar da kotunan da ake tankiya kan su a wuyan gwamnatin tarayya, ba jihohi ba.

Babban mai taya Buhari kokawa a Kotun Koli, kuma Antoni Janar na Tarayya, wato Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami, ya ce Dokar Musamman din da Buhari ya sa wa hannu a kan ka’ida ya yi, bai kauce wa ka’ida ba.

Malami ya ce Buhari ya yi amfani da Sashe na 5 na Kundin Tsarin Dokokin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Ya ce wanann sashe ya ba Shugaban Kasa ikon kirkiro Dokar Musamman a kan wasu muhimman bukatu na kuma ba a ce banda bangaren da ake tankiya a kai ba.

Su dai jihohi sun ce an dade su ke ciyar da kotunan kudaden da hakkin tarayya ne ta rika ba su,ba wai a rika ba su daga cikin kudaden jihohi ba.

Share.

game da Author