Kotu ta ce sanatan da ya mari mace a shagon sayar da kayan lalata, ya yi mata marin naira milyan 50

0

Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja ta yanke wa Sanata Elisha Abbo hukuncin biyan naira milyan 50 ga wata mata da ya falla wa mari a shagon sayar da sinadaran kara wa zinace-zinace armashi.

Matar mai suna Osinibira Warmate, Sanata Abbo ya ci zarafin ta ne a shagon sayar da zakarin roba da kayar badala a Maitama, Abuja, cikin 2019.

Lauya Nelson Onuoha, jagoran lauyoyin da su ka shigar da Sanatan kara a madadin matar, shi ne ya shaida wa PREMIUM TIMES haka a ranar Litinin.

Shi ma lauyan Sanata Abbo mai suna Abel Ozioko, shi ma ya shaida wa wakilin mu haka.

An dai kama Sanatan ne a kyamara, ya na gaura wa wata mari a shagon sayar da kayan lalata a Abuja.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin dambarwar bahallatsar Sanata Abbo, wanda rikici ya kaure dashi a shagon sayar da maganin karfin maza, a Abuja.

Mummunan lamarin ya faru bayan an yi zaben 2019, kafin a kai ga rantsar da sanatoci cikin Yuni,2011.

Sai dai bayan fitar bidiyon, Sanata Abbo nemi gafara a hannun batar, hakan bai hana an gurfanar da shi a Kotun Majastare da ke Zuba ba.

Kotun Majistare ta kori karar, amma kuma aka daukaka, inda a ka yanke hukuncin diyyar marin matar na naira milyan 50.

Share.

game da Author