KORONA: Za a bude makarantu ranar 14 ga Satumba a jihar Kogi

0

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewa za ta bude makarantun jihar ranar 14 ga Satumba.

Kwamishinan ilimin jihar Wemi Jones ya sanar da haka a garin Lokoja ranar Talata yana mai cewa gwamnan jihar Yahaya Bello da kansa ya tsaida wananan ranar.

Jones ya ce gwamnati za ta canja tsarin darussan da ake koyar wa dalibai a makarantun jihar saboda canjin da aka samu.

Ya yi Kira ga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, iyaye da sauran mutane da su hada hannu da gwamnati domin ganin an karantar da yara yadda ya kamata da kuma samar musu da kariya daga kamuwa da cutar Korona da wasu cututtukan.

A jihar Osun gwamnati ta ce za a bude makarantun boko ranar 21 ga Satumba.

Gwamnatin jihar Legas za ta bude jami’o’i da kwaleji kimiya da fasaha ranar 14 ga Satumba sannan a bude makarantun firamare da sakandare ranar 21 ga Satumba.

Share.

game da Author