Sakamako rahoton ‘Wordometer’ ya nuna cewa adadin yawan mutanen da cutar korona ya kashe a duniya ya kai miliyan daya.
A lissafe dai bisa ga rahoton mutum 1,000,502 ne suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.
Mutum 209,000 ne suka mutu a kasar Amurka, kasar Indiya dake bi mata nada mutum 95,000 da suka mutu.
Zuwa yanzu adadin yawan mutanen da Suka kamu da cutar a duniya ya kai mutum miliyan 33.
Duk da haka wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce akwai yiwuwar mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe basu a cikin lissafi saboda rashin bincike.
Ranar Asabar kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar cutar za ta kashe mutum miliyan 2 kafin a gano rigakafin ta.
Zuwa yanzu mutum miliyan 24 sun warke daga cutar a duniya.
Nahiyar Afrika
Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC ta bayyana cewa cutar korona ta kashe mutum 35,000 a Afrika.
Zuwa yanzu mutum miliyan 1.4 ne suka kamu da cutar a Afrika.
Kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun ce rashin yin gwajin cutar ne yake sa ba a iya tabbatar da adadin yawan wadanda suka kamu da wadanda suka mutu a Nahiyar ta Afrika.
A Najeriya mutum 58,324 suka kamu da cutar, 49,794 sun warke, 1,108 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,422 ke dauke da cutar.
Discussion about this post