Ministan harkokin mata da ci gaban al’umma Pauline Tallen ta bayyana cewa mata ne Korona ta fi yi wa illa a Najeriya fiye da maza.
Pauline ta fadi haka ne a taron tattauna daidaita jinsin maza ta mata domin a samu damawa da mata a harkokin gwamnati da ci gaban al’umman kasar nan.
Gidauniyar ‘Dinidari’ ne ta shirya wannan taro da aka yi ranar Litini.
Ta ce a lokacin da aka saka dokar Kulle, mata ne suka fi fadawa cikin kuncin rayuwa. Tace sanin kowa ne cewa mata da yawa sukan dan yi kasuwanci ne na yau da kullum. Rashin fita da ba sa iya yi ya talauta su da yawa.
A dalilin haka ne tace dole gwamnati da kungiyoyi su tallafa wa matan kasar nan.