Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 97 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –46, Kwara-12, Rivers-11, Adamawa-4, Niger-4, Ogun-4, Osun-4, Ekiti-3, Imo-3, Kaduna-3 Filato-2 da FCT-1
Yanzu mutum 57,242 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,569 sun warke, 1,098 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,575 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,943 FCT –5,551, Oyo – 3,231, Edo –2,611, Delta –1,799, Rivers 2,243, Kano –1,734, Ogun – 1,766, Kaduna –2,348, Katsina -849, Ondo –1,597, Borno –741, Gombe – 799, Bauchi – 689, Ebonyi –1,038, Filato -3,231 , Enugu – 1,234, Abia – 835, Imo – 562, Jigawa – 322, Kwara – 254, Bayelsa – 394, Nasarawa – 448, Osun – 817, Sokoto – 161, Niger – 254, Akwa Ibom – 288, Benue – 473, Adamawa – 234, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 75, Ekiti – 317, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.
Masana kimiya za su tabbatar sun fitar da maganin korona dake da inganci.
Masana kimiya dake aiki da kamfanonin sarrafa magunguna guda Tara sun yi alkawarin hadawa da samar da maganin rigakafin cutar korona da suka tabbatar da inganci da sahihancin sa.
Wadannan kamfanoni guda tara sun hada da AstraZeneca, BioNTech, GlaxoSmithKline, Johnson & Johnson, Merck, Moderna, Novavax, Pfizer da Sanofi.
Kamfanonin sun ce yanzu da duniya ta matsu a samar da maganin rigakafin cutar korona sun ce za su fitwr da maganin rigakafin ne bayan sun gudanar da gwaje-gwaje bisa ga sharuddan kimiya domin ganin maganin bai cutar da kiwon lafiyar mutane ba.