KORONA: Mutum 90 ne kacal suka kamu ranar Talata

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 90 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –33, Filato-27, Kaduna-17, Ogun-6, FCT-4, Anambra-1, Ekiti-1 da Nasarawa-1

Yanzu mutum 56,478 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 44,430 sun warke, 1,088 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,960 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,696 FCT –5,451, Oyo – 3,221, Edo –2,610, Delta –1,791, Rivers 2,208, Kano –1,732, Ogun – 1,754, Kaduna –2,296, Katsina -843, Ondo –1,583, Borno –741, Gombe – 773, Bauchi – 680, Ebonyi –1,034, Filato -3,142 , Enugu – 1,232, Abia – 828, Imo – 546, Jigawa – 322, Kwara – 1,002, Bayelsa – 393, Nasarawa – 447, Osun – 805, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 286, Benue – 467, Adamawa – 231, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 72 , Ekiti – 303, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.

Rahoton yadda cutar Korona ta talauta mutum milyan 37 talakawa fitik

Cutar Korona da ta barke a farkon shekarar 2020, ta maida mutum milyan 37 talakawa fitik, kamar yadda wani rahoto da Gidauniyar Tallafin Bill & Melida Foundation ta bayyana.

Gidauniyar ta ce mafi yawan wadanda suka afka cikin fatara da talauci sanadiyyar barkewar cutar, duk a kasashe masu tasowa su ke.

Cibiyar Goalkeepers 2020 ta ce bayan an shafe shekaru 20 cif ana samun raguwar fakiranci, yunwa da talauci a duniya, a yanzu kuma cutar Korona ta maida hannun agogo baya.

“Annobar Korona ta haddasa wa kimanin mutum milyan 37 fatara da talaucin da dukkan su babu mai hanyar samun dalar Amurka 1.9 a kullum.

“Dama kuma gejin ma’aunin fatara da talauci shi ne a ce magidanci ba ya iya samun dala 1.9 a kullum. To fakiranci ya kai shi makurar bango kenan.

“Wanda ke da sana’a ko aikin da ke iya samun dala 3.20 a kullum, su ne masu dan karamin karfin a samu a kashe wajen cin abincin yau da gobe. Su ma din kusan mutum milyan 68 duk sun afka cikin fatara da talauci, matakin ‘yan ‘ya mu samu, ya mu sa bakin mu’. Haka dai rahoton ya bayyana

Share.

game da Author