Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 216 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 20, Filato-59, Rivers-27, Abia-22, Oyo-18, Enugu-17, Kaduna-11, FCT-11, Ogun-10, Ebonyi-4, Osun-4, Ekiti-4, Delta-3, Edo-3, Akwa Ibom-2 da Bauchi-1
Yanzu mutum 54,463 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 42,439 sun warke, 1,027 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,997 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,177 , FCT –5,213, Oyo – 3,136, Edo –2,590, Delta –1,752, Rivers 2,168, Kano –1,727, Ogun – 1,669, Kaduna –2,163, Katsina –796, Ondo –1,543, Borno –741, Gombe – 723, Bauchi – 669, Ebonyi – 1,005, Filato -2,708, Enugu –1,179, Abia – 798, Imo – 529, Jigawa – 322, Kwara – 966, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 788, Sokoto – 159, Niger – 243, Akwa Ibom – 280, Benue – 460, Adamawa – 228, Anambra – 216, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 278, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.
Hanyoyin da uwa za ta iya shayar da danta nono Koda ta Kamu da korona.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa mace dake dauke da kwayoyin cutar Korona za ta iya shayar da danta nono yadda ya kamata ba tare da jaririn ya kamu da cutar ba.
WHO ta ce muddun Uwa ta kiyaye dokokin kare kai daga kamuwa da cutar Korona, to dan ta ba zai kamu ba don ta shayar dashi.
Kungiyar ta fadi haka ne domin karfafa gwiwowin mata wajen shayar da ‘ya’yan su nono akalla na tsawon watanni shida.
Ga hanyoyin
1. Uwa ta wanke hannayenta da ruwa da sabulu ko kuma da sinadarin tsaftace hannu kafin ta dauki da ko ‘yarta.
2. A yi amfani da takunkumin rufe fuska a duk lokacin da za a dauki ko shayar da da ko ‘ya nono.
3. A yi tari ko atishawa a gwiwar hannu ko kuma a yi amfani da tissue.
4. A tsaftace muhalli domin guje wa kamuwa da cututtuka.
5. Uwa za ta iya kiyaye sauran sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar koda bata da takunkumin rufe baki da hanci.
Discussion about this post