KORONA: Mutum 201 suka kamu da cutar a Najeriya ranar Laraba

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 201 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –77, Rivers 37, Filato 25, FCT 13, Kaduna 12, Ogun 12, Adamawa 8, Taraba 7, Imo 4, Kwara 2, Osun 2, Abia 1, Oyo 1.

Yanzu mutum 58,848 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 50,358 sun warke, 1,112 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,378 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,461, FCT –5,709, Oyo – 3,261, Edo –2,626, Delta –1,802, Rivers 2,395, Kano –1,737, Ogun – 1,850, Kaduna –2,419, Katsina -861, Ondo –1,631, Borno –745, Gombe – 883, Bauchi – 699, Ebonyi –1,040, Filato -3,450, Enugu – 1,289, Abia – 895, Imo – 572, Jigawa – 325, Kwara – 1,036, Bayelsa – 399, Nasarawa – 450, Osun –839, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 481, Adamawa – 248, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 102, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.

Yadda tsananta yin gwaji ya kawo raguwar yaduwar cutar a Najeriya

Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta yi game da yaduwar cutar Korona a kasar nan ya nuna Najeriya ta fara samun raguwar yaduwar cutar.

An gano alamun wannan raguwa ne a cikin watanni biyar da suka gabata.

Sakamakon bincike ya nuna cewa daga ranar Lahadi 13 zuwa Asabar 19 ga Satumba mutum 968 suka kamu sannan a makon da ya gabata mutum 1,272 ne suka kamu a kasar nan.

Rahotanin hukumar NCDC ya nuna cewa ranar 19 ga Afrilu da 25 ga Mayu ne Najeriya ta Samu irin wannan raguwar yaduwar cutar tun da cutar ta bullo a kasan.

Inganta yin gwajin cutar

Rahotanni sun nuna cewa inganta yi wa mutane gwajin cutar na daga cikin dalilan da ya sa kasan ta samu nasarar rage yaduwar cutar.

A makon da ya gabata mutum 31,943 ne aka yi wa gwajin wanda haka ya nuna cewa an samu karin kashi 50 daga mutum 16,935 din da aka yi wa gwajin cutar a makon baya.

Sannan a cikin makonni hudu da suka gabata mutum kasa da 2,000 ne suka kamu da cutar a fadin kasar na.

Duk da haka kwamitin yaki da cutar korona ta kass ta ci gaba da jadaddawa mutane kan kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author