Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 195 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –39, Enugu-51, Gombe-40, Filato-23, FCT-15, Rivers-12, Kaduna-8, Ondo-3, Bauchi-2, Edo-1 da Ogun-1
Yanzu mutum 57,437 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,674 sun warke, 1,100 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,663 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,982, FCT –5,566, Oyo – 3,231, Edo –2,612, Delta –1,799, Rivers 2,255, Kano –1,734, Ogun – 1,767, Kaduna –2,356, Katsina -849, Ondo –1,600, Borno –741, Gombe – 839, Bauchi – 691, Ebonyi –1,038, Filato -3,254 , Enugu – 1,285, Abia – 835, Imo – 562, Jigawa – 322, Kwara – 254, Bayelsa – 394, Nasarawa – 448, Osun – 817, Sokoto – 161, Niger – 254, Akwa Ibom – 288, Benue – 473, Adamawa – 234, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 75, Ekiti – 317, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.
Tsananta yin gwaji ya rage yaduwar cutar korona a cikin watanni biyar da suka wuce
Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta yi game da yaduwar cutar Korona a kasar nan ya nuna Najeriya ta fara samun raguwar yaduwar cutar.
An gano alamun wannan raguwa ne a cikin watanni biyar da suka gabata.
Sakamakon binciken ya nuna cewa daga ranar Lahadi 13 zuwa Asabar 19 ga Satumba mutum 968 ne suka kamu sannan a makon da ya gabata kuwa mutum 1,272 ne suka kamu a kasar nan.
Rahotanin hukumar NCDC ya nuna cewa ranar 19 ga Afrilu da 25 ga Mayu ne Najeriya ta Samu irin wannan raguwar yaduwar cutar tun da cutar ta bullo a kasan.
Inganta yin gwajin cutar
Rahotanni sun nuna cewa inganta yi wa mutane gwajin cutar na daga cikin dalilan da ya sa kasan ta samu nasarar rage yaduwar cutar.
A makon da ya gabata mutum 31,943 ne aka yi wa gwajin wanda haka ya nuna cewa an samu karin kashi 50 daga mutum 16,935 din da aka yi wa gwajin cutar a makon baya.
Sannan a cikin makonni hudu da suka gabata mutum kasa da 2,000 ne suka kamu da cutar a fadin kasar na.
Duk da haka kwamitin yaki da cutar korona ta kass ta ci gaba da jadaddawa mutane kan kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar.
Discussion about this post