Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 136 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –71, Rivers-23, Filato-12, Adamawa-6, Oyo-6, Kaduna-5, Abia-3, FCT-3, Katsina-2, Kwara-2, Bauchi-1, Borno-1, da Edo-1
Yanzu mutum 58,460 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 49,895 sun warke, 1,111 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,454 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,310, FCT –5,677, Oyo – 3,260, Edo –2,625, Delta –1,802, Rivers 2,370, Kano –1,737, Ogun – 1,836, Kaduna –2,402, Katsina -859, Ondo –1,631, Borno –742, Gombe – 864, Bauchi – 699, Ebonyi –1,040, Filato -3,400, Enugu – 1,289, Abia – 894, Imo – 568, Jigawa – 325, Kwara – 1,034, Bayelsa – 398, Nasarawa – 449, Osun – 827, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 481, Adamawa – 234, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.
An rufe wuraren kula da masu Korona biyu a Abuja
Gwamnati ta rufe wuraren kula da masu Korona biyu daga cikin hudu da ake da su a Abuja saboda duk kowa ya warke.
Gwamnati ta rufe wuraren ne saboda rashin babu wasu masu fama da cutar da za a ajiye su a wuraren.
An rufe wuraren da aka bude dake Karu da Asokoro.
A yanzu dai wuraren kula da masu Korona dake Idu da THISDAY Dome ne suka rage a Abuja.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 126 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.