KORONA: Mutum 136 suka kamu da cutar a Najeriya ranar Asabar

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 136 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –41, Ogun-27, Rivers-19, Abia-10, Oyo-6, Filato-6, Bauchi-5, Ondo-5, Ekiti-4, Kaduna-4, Edo-3, Ebonyi-2, Bayelsa-1, Delta-1, Osun-1 da Yobe-1.

Yanzu mutum 58,198 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 49,722 sun warke, 1,106 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,370 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,215, FCT –5,644, Oyo – 3,254, Edo –2,623, Delta –1,802, Rivers 2,324, Kano –1,737, Ogun – 1,823, Kaduna –2,393, Katsina -849, Ondo –1,625, Borno –741, Gombe – 864, Bauchi – 697, Ebonyi –1,040, Filato -3,379, Enugu – 1,289, Abia – 891, Imo – 566, Jigawa – 325, Kwara – 1,028, Bayelsa – 398, Nasarawa – 449, Osun – 827, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 481, Adamawa – 234, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.

Kashi 10% na wadanda suka kamu da Korona a Najeriya yan kasa da shekara 19 ne.

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce Kashi 10 bisa 100 na wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yan kasa da shekara 19 ne.

Ehanire ya fadi haka ne a taron da kwamitin yaki da cutar korona ya yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.

Ya ce kimiyya ya nuna cewa tsofaffi musamman wadanda ke da shekaru sama da 60 sun fi saurin kamuwa da cutar.

Ya Kuma ce wadannan mutane na daga cikin rukunin mutanen dake dauke da cutar ba tare da sun nuna alamun cutar ba wanda hakan ya sa za so iya yada cutar ba tare da sun sani ba.

Ministan ya yi kira ga masu makarantu da iyaye da su zage damtse wajen kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare ‘ya’yan su a lokacin da za a bude makarantu.

Inganta yin gwajin cutar

Ehanire ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi Kan hada hannu da hukumar NCDC domin yaki da cutar.

“Mutanen dake fama da alamun zazzabin cizon sauro,rashin iya shakan kashi ko dandano, mutanen da suka Yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar, tsofaffi, wadanda ke dauke da wasu cututtuka a jikinsu da matafiya na cikin mutanen da ya kamata ya zage damtse wajen yi wa gwajin cutar.

Bayan haka Ehanire ya ce gwamnatin kasar Amurka ta tallafa wa Najeriya da na’urorin taimakawa numfashin mara lafiya.

Ya ce gwamnatin kasar Amurka za ta horas da ma’aikatan lafiyan dake manyan asibitocin kasar nan yadda za su yi amfani da na’urorin.

Sannan gwamnatin Najeriya za ta horas da ma’aikatan lafiya dake sauran asibitocin kasar nan.

Mutum 57,437 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,674 sun warke, 1,100 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,663 ke dauke da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author