KORONA: Mutum 131 suka kamu ranar Laraba, Yanzu mutum 56,735 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 131 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –45, Kaduna-17, Filato-17, FCT-16, Delta-6, Niger-6, Kwara-5, Oyo-3, Akwa Ibom-2, Cross River-2, Ekiti-2, Enugu-2, Osun-2, Sokoto-2, Bauchi-1, Ebonyi-1, Katsina-1 da Rivers-1.

Yanzu mutum 56,735 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,092 sun warke, 1,093 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,550 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,768 FCT –5,504, Oyo – 3,226, Edo –2,610, Delta –1,799, Rivers 2,209, Kano –1,733, Ogun – 1,755, Kaduna –2,322, Katsina -845, Ondo –1,590, Borno –741, Gombe – 779, Bauchi – 682, Ebonyi –1,035, Filato -3,175 , Enugu – 1,234, Abia – 835, Imo – 551, Jigawa – 322, Kwara – 1,009, Bayelsa – 393, Nasarawa – 447, Osun – 807, Sokoto – 161, Niger – 250, Akwa Ibom – 288, Benue – 467, Adamawa – 231, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 73, Ekiti – 307, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.

Yadda ‘Yan Kasar waje ke shigowa Najeriya da takardun gwajin cutar na karya

Kodinatan kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Korona Sani Aliyu ya bayyana cewa ‘yan kasar waje na shigowa Najeriya da takardar sakamakon gwajin cutar korona na karya.

Aliyu ya ce irin wadannan mutane Idan an yi musu gwajin cutar sakamakon gwajin kan nuna suna dauke da kwayoyin cutar a jikinsu.

Ya fadi haka ne a zaman da kwamitin ta yi domin tattauna zirga-zirgar jiragen Sama na kasa-da-kasa ranar Talata a Abuja.

Aliyu ya ce an gano mutane irin haka daga kasashe 13 inda daga cikinsu an gano mutum tara na dauke da cutar.

Idan ba a manta ba a ranar biyar ga Satumba ne gwamnati ta dawo da zirga-zirgar jiragen Sama na kasa-da-kasa a kasar nan.

Aliyu ya ce domin kawar da irin wadannan matsaloli gwamnati ta canja wasu sassa dokar shigowa Najeriya a lokacin Korona.

Wuraren yin gwajin cutar

Shugaban kwamitin sufurin jiragen sama na majalisar dattawa Smart Adeyemi ya dora laifin gabatar da sakamakon gwajin cutar korona na boge akan rashin kyale asibitocin gwamnati su rika yin gwajin cutar da tsadan yin gwajin cutar.

Adeyemi ya ce rage kudin yin gwajin cutar da yardawwa asibitocin gwamnati su rika yi wa mutane gwajin cutar zai taimaka wajen kawar da wadannan matsaloli da ake fama da su.

Kwamitin ya dora wa ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire da Aliyu nauyin ganin asibitocin gwamnati sun fara yi wa mutane gwajin cutar sannan da tabbatar da cewa an rage kudin yin gwajin cutar.

Share.

game da Author