Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 111 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –31, Gombe-18, Kaduna-18, FCT-15, Rivers-14, Imo-3, Kwara-3, Oyo-3, Bayelsa-2, Ogun-2, Edo-1, Osun-1
Yanzu mutum 57,724 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,985 sun warke, 1,102 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,637 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,086, FCT –5,598, Oyo – 3,236, Edo –2,616, Delta –1,800, Rivers 2,277, Kano –1,734, Ogun – 1,774, Kaduna –2,377, Katsina -849, Ondo –1,606, Borno –741, Gombe – 857, Bauchi – 692, Ebonyi –1,038, Filato -3,304 , Enugu – 1,285, Abia – 835, Imo – 565, Jigawa – 322, Kwara – 1,028, Bayelsa – 397, Nasarawa – 449, Osun – 818 , Sokoto – 161, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 473, Adamawa – 234, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 75, Ekiti – 317, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.
Korona ta fi yin Illa ga mata fiye da maza
Ministan harkokin mata da ci gaban al’umma Pauline Tallen ta bayyana cewa mata ne Korona ta fi yi wa illa a Najeriya fiye da maza.
Pauline ta fadi haka ne a taron tattauna daidaita jinsin maza ta mata domin a samu damawa da mata a harkokin gwamnati da ci gaban al’umman kasar nan.
Gidauniyar ‘Dinidari’ ne ta shirya wannan taro da aka yi ranar Litini.
Ta ce a lokacin da aka saka dokar Kulle, mata ne suka fi fadawa cikin kuncin rayuwa. Tace sanin kowa ne cewa mata da yawa sukan dan yi kasuwanci ne na yau da kullum. Rashin fita da ba sa iya yi ya talauta su da yawa.
A dalilin haka ne tace dole gwamnati da kungiyoyi su tallafa wa matan kasar nan.