KORONA: Mutum 100 cif suka kamu ranar Lahadi a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 100 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -39, FCT-22, Kaduna-19, Oyo-7, Ebonyi-6, Edo-3, Katsina-1, Ekiti-1, Bauchi-1 da Nasarawa-1

Yanzu mutum 55,005 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 43,013 sun warke, 1,057 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 10,935 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,347 , FCT –5,301, Oyo – 3,194, Edo –2,597, Delta –1,768, Rivers 2,175, Kano –1,727, Ogun – 1,678, Kaduna –2,208, Katsina –813, Ondo –1,561, Borno –741, Gombe – 744, Bauchi – 670, Ebonyi – 1,020, Filato -2,720, Enugu –1,184, Abia – 807, Imo – 534, Jigawa – 322, Kwara – 982, Bayelsa – 391, Nasarawa – 438, Osun – 795, Sokoto – 159, Niger – 244, Akwa Ibom – 280, Benue – 460, Adamawa – 228, Anambra – 221, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 283, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 83.

Masu firgita mutane ke kashe masu cutar Korona -Inji Shugaban CAN bayan ya warke

Makonni biyu bayan sanarwar cewa Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Jihar Adamawa, Stephen Mamza ya kamu da cutar Coronavirus, an bayyana warkewar sa har ma an sallame shi daga cibiyar killace masu fama da cutar.

A wani taro da manema labarai da ya yi a Yola, Mamza wanda kuma shi ne Babban Limamin Darikar Katolika na Adamawa, ya gode wa Allah da sauran jama’a da kuma jami’an kiwon lafiya da suka rika kula da shi.

Sai dai kuma ya bayyana cewa cutar Coronavirus ba abin tayar da hankali ba ce. Kawai dai ana firgita mutane, a na kara zuzuta ta fiye da yadda ta ke.

Share.

game da Author