Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 176 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –73, Filato-50, FCT-17, Rivers-8, Ondo-6, Niger-5, Ogun-5, Edo-3, Kaduna-3, Oyo-2, Bauchi-1, Bayelsa-1, Delta-1 da Nasarawa-1
Yanzu mutum 57,613 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 48,836 sun warke, 1,100 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,677 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,055, FCT –5,583, Oyo – 3,233, Edo –2,615, Delta –1,800, Rivers 2,263, Kano –1,734, Ogun – 1,772, Kaduna –2,359, Katsina -849, Ondo –1,606, Borno –741, Gombe – 839, Bauchi – 692, Ebonyi –1,038, Filato -3,304 , Enugu – 1,285, Abia – 835, Imo – 562, Jigawa – 322, Kwara – 254, Bayelsa – 395, Nasarawa – 449, Osun – 817, Sokoto – 161, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 473, Adamawa – 234, Anambra – 232, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 75, Ekiti – 317, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 85.
Kashi 10% na wadanda suka kamu da Korona a Najeriya yan kasa da shekara 19 ne
Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce Kashi 10 bisa 100 na wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yan kasa da shekara 19 ne.
Ehanire ya fadi haka ne a taron da kwamitin yaki da cutar korona ya yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.
Ya ce kimiyya ya nuna cewa tsofaffi musamman wadanda ke da shekaru sama da 60 sun fi saurin kamuwa da cutar.
Ya Kuma ce wadannan mutane na daga cikin rukunin mutanen dake dauke da cutar ba tare da sun nuna alamun cutar ba wanda hakan ya sa za so iya yada cutar ba tare da sun sani ba.
Ministan ya yi kira ga masu makarantu da iyaye da su zage damtse wajen kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare ‘ya’yan su a lokacin da za a bude makarantu.