Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 239 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 19, Filato -116, FCT-33, Ekiti-12, Kaduna-11, Ogun-11, Ebonyi-8, Benue-7, Abia-5, Delta-5, Ondo-4, Edo-3, Imo-2, Osun-2 da Bauchi-1
Yanzu mutum 54,247 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 42,010 sun warke, 1,023 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,214 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 18,157 , FCT –5,202, Oyo – 3,118, Edo –2,587, Delta –1,749, Rivers 2,141, Kano –1,727, Ogun – 1,659, Kaduna –2,152, Katsina –796, Ondo –1,543, Borno –741, Gombe – 723, Bauchi – 668, Ebonyi – 1,001, Filato -2,649, Enugu –1,162, Abia – 776, Imo – 529, Jigawa – 322, Kwara – 966, Bayelsa – 391, Nasarawa – 434, Osun – 784, Sokoto – 159, Niger – 243, Akwa Ibom – 278, Benue – 460, Adamawa – 228, Anambra – 216, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 67, Ekiti – 274, Taraba- 87, Kogi – 5, da Cross Rivers – 82.
Hanyoyin kiyaye wa daga kamuwa da cutar Korona
Sakamakon binciken da hukumar dakile yaƴuwar cututtuka ta kasa NCDC ta gabatar na mako-mako ya nuna cewa an fara samun ragowa a adadin yawan mutanen dake kamuwa da cutar.
Hakan na nuna cewa akwai alamun samun raguwar yaduwar cutar.
A dalilin haka be gwamnatin tarayya ta Yi Kira ga mutanen kasar nan da su kara zage damtse wajen kiyaye sharaddun guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Akan kama cutar be a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.