KORONA: An rufe wuraren kula da masu Korona biyu a Abuja

0

Gwamnati ta rufe wuraren kula da masu Korona biyu daga cikin hudu da ake da su a Abuja saboda duk kowa ya warke.

Gwamnati ta rufe wuraren ne saboda rashin babu wasu masu fama da cutar da za a ajiye su a wuraren.

An rufe wuraren da aka bude dake Karu da Asokoro.

A yanzu dai wuraren kula da masu Korona dake Idu da THISDAY Dome ne suka rage a Abuja.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 126 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –24, FCT-30, Rivers-23, Ogun-13, Katsina-9, Filato-9, Ondo-6, Kaduna-4, Kwara-4, Imo-2, Bauchi-1 da Edo-1.

Yanzu mutum 58,324 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 49,794 sun warke, 1,108 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,422 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 19,239, FCT –5,674, Oyo – 3,254, Edo –2,624, Delta –1,802, Rivers 2,347, Kano –1,737, Ogun – 1,836, Kaduna –2,397, Katsina -857, Ondo –1,631, Borno –741, Gombe – 864, Bauchi – 698, Ebonyi –1,040, Filato -3,388, Enugu – 1,289, Abia – 891, Imo – 568, Jigawa – 325, Kwara – 1,032, Bayelsa – 398, Nasarawa – 449, Osun – 827, Sokoto – 162, Niger – 259, Akwa Ibom – 288, Benue – 481, Adamawa – 234, Anambra – 237, Kebbi – 93, Zamfara – 78, Yobe – 76, Ekiti – 321, Taraba- 95, Kogi – 5, da Cross Rivers – 87.

Share.

game da Author