Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji na Jihar Kaduna ta rufe wasu manya-manyan gidajen buga cacan kwallon kafa da ke jihar.
Hukumar ta ce gwamnatin jihar na bin wadannan gidajen buga cacan kwallon kafa dake kasuwanci a jihar da suka hada da Betnaija, BetKing, Acesss Bet da sauransu miliyoyin kuɗi.
Shugaban sashen kula da gidajen buga wasannin caca, Liye Anthony ya bayyana cewa akwai akalla gidajen cacan kwallon kafa 1500, kuma za su bisu daya bayan daya su garƙame saboda basu da cikakken rajista da gwamnatin jihar sannan ana bin wasunsu miliyoyin kuɗin haraji da basu biya ba.
Shugaban hukumar Zaid Abubakar, ya shaida cewa gwamnati na bin gidaje cacan sama da naira miliyan 500.
” Kamfanin KC wanda sune ke da mallakin fitaccen gidan buga cacan kwallon kafa, na Bet9ja muna binsu naira miliyan 324 kudin haraji, BetKing kuma naira miliyan 68 sai kuma access bet naira miliyan 33.
Ya kara da cewa gidajen caca a jihar na samu akalla naira biliyan 2 duk wata amma basu biyan kudin haraji.
Sannan kuma Abubakar ya ce kadin mutum ya bude gidan caca irin haka, sai yaya biya kudin rajista har naira 400,000, kafin nan a fara duba yiwuwar yi masa rajista a jihar.
Matasa har da manya sun raja’a matuka wajen buga irin wannan wasanni.
Da yawa suna samun nasarar cin kudade masu yawa saidai kuma da waya suna hasara ne kawai.
Kamar yadda kamfanonin ke da shaguna da ake zuwa buga wannan wasa, haka zaka iya buga shi ta yanar gizo.