Kotu dake Ile-Tuntun, jihar Oyo ta warware auren dake tsakanin Ibukun Amosun da Babatundea dalilin karambanin mahaifin maigida.
Ibukun Amosun ta shigar da kara a kotu domin kotu ta raba auren ta da mijinta Babatunde.
Ibukun ta ce ta gaji da irin zaman auren da take yi da Babatunde domin tsakanin ta da minjin ta babu sirri kuma mijin nata bashi da ikon yanke hukunci a cikin gidansa a matsayinsa na maigida.
“Kafin mu yi aure Babatunde ya yi alkawarin barina na yi aiki a duk garin da na samu aiki da hakan ya sa nake aiki a jihar Legas.
“Bayan wani lokaci da fara aikin sai Babatunde ya ce yana bukatar na bar aikin da nake yi in dawo gida na zauna.
“Babatunde ya canja ra’ayinsa ne bayan ya tattauna da mahaifinsa da ya umarce sa ya sallame ni idan naki amincewa wa.
A zaman da aka yi a kotun Babatunde bai zo kotun ba amma mahaifinsa Johnson ya bayyana a madadin dansa.
Johnson ya yi bayanin cewa sun gaji da munanan halaiyan Ibuku musamman yadda mahaifiyar ta ke ziga ta maimakon ta kwabe ta.
“Ibukun ta ki zama da mijinta a gida daya wanda bisa ga al’adun mu na hakan bai dace ba.
“Sannan Ibukun ta ki ta haihu saboda tana bautar kasa.
Mahaifiyar Ibuku ta koka kan cewa yin katsalandan da mahaifin Babatunde ya ke yi shine ya dagula zaman Ibukun da mijinta.
A karshe dai Alkalin kotun ya raba auren, kowa ya kama gaban sa.