Kasafin kuɗin da Najeriya ta ware wa muhimman ayyukan gona bai kai kashi 2% bisa 100% ba -Wani Jami’i

0

Wani Jami’in Gudanar da Kasafin Kudaden Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya (FMARD), ya tabbatar da cewa kasafin da gwamnatin tarayya ta ware wa muhimman ayyukan gona bai kai kashi 2% bisa 100% ba.

Jami’in mai suna Okosor Oyere, ya bayyana haka lokacin da ya ke gabatar da na sa bayanin a wurin Taron Masu Hakki a Harkokin Noma da aka kammala a kan Makomar Noma a Karkashin Kasafin 2021.

A taron na kwanaki biyu da aka yi a Lagos, a ranakun 23 da 24 Ga Satumba, Kungiyar ActionAid Nigeria ce ta shirya shi, tare da hadin-guiwar ONE Campaign, Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare da kuma Sashen Inganta Harkokin Noma da Ruwan Sha na Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Taron ya samu albarkacin mahalarta 163.

Kasafin Ayyukan Noma Ya Yi Kadan -Oyere

Oyere ya ce karancin kudaden da ake warewa wajen manyan ayyukan noma sun yi karancin da ke haifar da kasa gudanar da manyan ayyuka da kuma barin wasu kwantai na wasu ayyuka masu matukar muhimmanci.

Ya ce a Yarjejeniyar Makabo ta 2014 da Shugabannin Afrika su ka rattaba wa hannu, sun amince cewa duk shekara kowace kasar Afrika za ta rika kashe kashi 10% bisa 100% na kasafin kudaden shekarar a fannin noma.

An dai shirya taron ne domin mahalarta taron su fahimtar da Najeriya a fahimci tsare-tsaren harkokin noman ta da inda ya ke da dangantaka da kusantaka da Tsare-tsaren Bunkasa Harkokin Noma na Afrika (CAACP), da kuma muradun da CAADP din ke son cimmawa.

Kasashen Afrika dai sun cimma Yarjejeniyar Malabo ce a 2014 domin bunkasa harkokin noma, inda su ka yi kintacen cewa idan kowace kasa ta rika kashe akalla kashi 10% bisa 100% na kasafin kudin ta na shekara a fannin noma, to zuwa 2025 Nahiyar Afrika za ta zama kasaitacciyar nahiya mai yalwar noma da kuma yin bankwana da barazanar yunwa.

Share.

game da Author