KARIN FARASHIN FETUR: Tausayi ya sa aka bar shi naira 161, amma kamata ya yi a kara zuwa naira 182 – Gwamnatin Buhari

0

Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa tsananin tausayin ‘yan Najeriya ya sa aka kara farashin fetur zuwa naira 161, amma naira 181 ya kamata a kara farashin litar fetur.

Wannan furuci ya fito daga bakin Karamin Ministan Harkokin Fetur, Timipre Sylva, a taron ganawa tsakanin tawagar gwamnatin tarayya da kuma shugabannin Kungiyar Kwadago ta Kasa, da aka yi ranar Talata a Abuja.

Gamayyar Kungiyar Kwadago ta Kasa dai ta nemi gwamnati ta janye karin kudin fetur, ko kuma a tafi yajin-aikin da tsaida harkokin gwamnati gaba daya.

A kan haka ne ake ta tsallen-gada tsakanin jami’an gwamnati, inda ake nuna wa Kungiyar Kwadago dalilan karin kudin fetur din.

Sylva ya ce gwamnatin tarayya ba ta iya jure biyar manyan dillalan da ke shigo da fetur kudin tallafin mai, wato ‘subsidy’.

Don haka ne aka kara kudin fetur saboda an daina biyan kudaden tallafin.

“Maganar gaskiya ba ma kari zuwa naira 161 ya kamata a ce an yi ba. Kamata ya yi a ce an kara zuwa naira 181.

“Amma da Shugaba Buhari ya duba, sai ya ce a bar shi a naira 161 din.” Haka Sylva ya shaida wa shugabannin na Kungiyar Kwadago, tare da rokon ‘yan Najeriya su jure kawai a tafi a haka.

“Daga 2016 zuwa 2019 gwamnati ta biya naira tiriliyan 10 kudin talllafin mai. A kowace rana gwamnati na biyan kudin tallafin mai naira bilyan daya, daga 2016 zuwa 2019.

“To amma yanzu an janye bayar da tallafin. Kuma ana bada musayar kudaden waje a kan kowace dala daya kan naira 390, maimakon naira 450 da ake sayarwa a kasuwar-tsaye.”

Bayanan Sylva dai sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta yi baki-biyu dangane da karin kudin litar fetur.

Da farko gwamnati cewa ta yi ta tsame hannun ta daga yanka wa litar mai farashi. Ko wannan kari da aka yi zuwa 161, cewa ta yi ‘yan kasuwa ne su ka yi karin ba gwamnati ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin inda Gwamnati ta ce ta tsame hannun ta daga yanka farashin litar fetur, kowane mai gidan mai ya saida ferur a farashin da zai iya fita kawai.

Gwamnatin Tarayya ta tsame hannun ta daga yanka farashin litar man fetur a Najeriya, ta na mai cewa daga yanzu kowane dillalin ferur zai iya saidawa a farashin da ya ga zai iya cin riba kawai.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Hukumar Kayyade Farashin Fetur da Gas ta Kasa (PPPRA).

“Daga yanzu babu sauran kayyade farashi, kowane dillalin mai ya fita ya samo mai duk inda zai iya sayowa. Kuma ya saida man sa a farashin da ya yi masa daidai.

“Gwamnati ta tsame hannun ta a sha’anin kayyade farashin litar fetur a kasar nan. Amma za ta rika sa-ido domin tabbatar da cewa masu gidajen mai ba su wuce-gona-da-iri ba”

Hukumar PPPRA ta bayyana tsame hannun ta daga kayyade farashin litar man fetur, kamar yadda dama Karamin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya taba fada cikin watan Afrilu cewa gwamnati za ta janye hannun ta daga kayyade farashin litar fetur.

Babban Sakataren Hukumar Kayyade Farashin Fetur, Abdullahi Sa’idu ne ya bayyana janye hannun hukumar daga kayyade farashin litar fetur.

Wannan katan-katana ta taso tun cikin watan Maris lokacin da farashin danyen mai ya karye a kasuwar duniya, Najeriya ta rasa isassun kudaden shiga.

Farkon Satumba gwamnati ta janye tallafin fetur, wanda a sanadiyyar haka litar fetur ta karu.

Karin kudin ferur ya zo daidai da karin kudin wutar lantarki da kuma yanayi na masifar tsadar rayuwar da ta haddasa tsadar kayan abinci.

Yayin da ake tsakiyar caccakar gwamnatin Buhari, ya fito ya ce karin kudin fetur ya zauna daram, domin idan ba a kara kudin ba, to saboda karancin kudaden shiga, Najeriya za ta iya shiga mawuyacin hali.

Tuni dai a wasu jihohi aka fara zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin fetur da na wutar lantarki.

Kungiyoyin kwadago da na dalibai da sauran jama’a na ta kiraye-kirayen cewa ba za su amince da karin kudin ba.

Shugaba Buhari ya hau mulki bayan ya yi wa ‘yan Najeriya alkawarin za a rika sayen litar fetur naira 45 a maimakon naira 89 da ta ke a lokacin, karkashin mulkin Jonathan.

Sai dai kuma tun bai yi nisa ba aka yi wani mahaukacin karin kudin litar fetur zuwa naira 145.

Share.

game da Author